Sai mun kayar da shi: Jam'iyyun siyasa 34, yan takara 20 sun hada kai domin ganin karshen gwamnan jihar Bauchi

Sai mun kayar da shi: Jam'iyyun siyasa 34, yan takara 20 sun hada kai domin ganin karshen gwamnan jihar Bauchi

Wata gamayyar jam'iyyun siyasa 33 da yan takara 20 sun lashi takobin ganin bayan gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, ta hanyar goyon bayan dan takaran jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Senator Bala Abdulkadir.

Shugaban gamayyar, Muhammadu Bello Kirfi, ya bayyana cewa sun hada wannan gamayya ne domin ganin cewa gwamnan jihar ya fadi a zaben 2019 da zai gudana ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Ya kara da cewa sun yanke shawara zaben tsohon ministan birnin tarayya na PDP saboda shi keda karfi kayar da gwamna Abubakar a zaben.

Saboda haka, yana kira ga jama'ar jihar da masu ruwa da tsaki su zabi Sanata Bala Mohammed.

Game da cewarsa, mutanen jihar Bauchi sun amince da shugaba Muhammadu Buhari kuma hakan yasa suka zabeshi a zaben shugaban kasa, amma mutanen jihar Bauchi basu jin dadin mulkin gwamnan jihar, Abubakar.

Jam'iyyun da suka hada kan sune United Progressive Party (UPP), Green Party of Nigeria (GPN), Change Advocacy Party (CAP), All Peoples Movement (APM), All Blending Party (ABP), Peoples Democratic Party (PDP), Action Joint Alliance (MAJA), Advance Peoples Democratic Alliance (APDA), Grassroot Development Party of Nigeria (GDPN), Accord Party (AP) da Independent Democrats (ID).

Daga cikinsu akwai All Grands Alliance Party (AGAP), New Generation Party (NGP), Nigeria Peoples Congres (NPC), Legacy Party of Nigeria (LPC), Mordern Democratic Party (MDP), New Progressive Movement (NPM) and Providence Peoples Congress (PPC).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel