Zaben gwamna: Malaman makarantun Kaduna sun jaddada goyon baya ga El-Rufai

Zaben gwamna: Malaman makarantun Kaduna sun jaddada goyon baya ga El-Rufai

Akalla malaman makarantun firamari guda dubu goma ne suka halarci gangamin taron addu’o’I na musamman domin samun nasarar gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai a zaben gwamnoni da zai gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Malaman sun fito ne daga kananan hukumomi takwas na Sanatoriya ta Arewacin Kaduna, inda suka taru a makarantar Firamari ta Hanwa GRA dake karamar hukumar Sabon gari cikin garin Zariya.

KU KARANTA: An bude asusun neman taimako dan taimaka ma Atiku ya kai karar Buhari gaban kotu

Zaben gwamna: Malaman makarantun Kaduna sun jaddada goyon baya ga El-Rufai
Malaman
Asali: UGC

Wanda ya shirya gangamin, Malam Danladi Umar Abdullahi ya bayyana makasudin shirya wanna taro, inda yace manufar taron shine bayyana goyon bayansu ga El-Rufai, tare da nuna amincewarsu a gareshi na ya zarce akan mukaminsa.

“Dalilin taruwarmu anan shine don nuna godiya ga Allah bisa ni’imar da yayi mana, tare da gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya a Kaduna da ma kasa gaba daya. Haka zalika mun hadu anan ne don yabawa da hangen nesan Gwamna El-Rufai ta yadda ya tsaftace sha’anin karatu a jahar.

“Muna fatan Allah Ya bashi nasara a zabe mai zuwa, domin nasararsa it ace nasarar jama’an jahar Kaduna don hakan zai bashi damar inganta ilimi a jahar. Kamar yadda kuke gani adadinmu yah aura dubu goma.

“Kuma mun kunshi tsofaffin Malamai da sababbin da El-Rufai ya dauka, kuma hakan ya burgemu matuka ta yadda tsofaffin malaman ma suka shigo cikinmu domin sun san ilimi ya bunkasa a jahar Kaduna, saboda a yanzu haka dan aji uku yana jin turanci.

Daga karshe Danladi ya shawarci gwamnan jahar Kaduna daya cigaba da kokarin da yake na inganta sha’anin ilimi a jahar Kaduna ta hanyar horas da Malamai daga lokaci zuwa lokaci, inda yace hakan zai kara ma Malamai kwazo, tare da basu sabbin dabarun koyarwa.

Idan za’a tuna a shekarar 2017 ne gwamnan ya sallami gurbatattun malaman firamari 21,780 da suka gagara cin jarabawar dalibai yan aji hudu da gwamnatin ta shirya musu, kuma tuni gwamnatin ta fara aikin daukan sabbin Malamai 25,000 don maye gurbinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel