Ka fadi a ina ka yi karatun injiniyan da ake ma ka lakabi da shi - Ganduje ya farke wa Kwankwaso laya

Ka fadi a ina ka yi karatun injiniyan da ake ma ka lakabi da shi - Ganduje ya farke wa Kwankwaso laya

A yau, Laraba, ne gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kalubalanci tsohon gwamna kuma sanata mai barin gado, madugun Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso, da ya nuna shaidar takardar karatun injiniya da ake ma sa lakabi da shi.

Ganduje, a cikin jawabin da sakataren sa na watsa labarai, Abba Anwar, ya fitar, ya ce, “a ina ya yi karatun zama injiniya? Na kalubalance shi. Hatta jarrabawar kamala karatun makarantar firamare faduwa ya yi.

saboda ya kasa cin jarrabawa ne aka kai shi makarantar koyon kanikanci. Kowa ya san cewae sai wanda bai ci jarrabawa ba ake kai wa irin wadannan makarantu.

Ganduje ya yi wanannan furuci ne yayin rantsar da kwamitin da zai biya daliban jihar Kano da ke karatu a gida Najeriya kudaden tallafi, wanda aka yi a dakin taron na ‘Ante-Chamber’ da ke gidan gwamnati a yau, Laraba.

Ka nuna wa duniya takardar shaidar kai injiniyan gaske ne – Ganduje ya caccaki Kwankwaso
KGanduje
Asali: Depositphotos

Mai karancin ilimi ne kawai zai yi abinda Kwankwaso ya yi ilimi a jihar Kano lokacin mulkin sa,” a cewar Ganduje.

A cewar Ganduje, Kwankwaso ya kasa fito da tsarin inganta ilimi a jihar Kano ne saboda rashin ilimin sa.

DUBA WANNAN: Sarakunan gargajiya sun ziyarci Buhari domin taya shi murna, hotuna

Shi gani ya ke ya fi kowa waye wa, haka yak e daukan kan sa. Tsarin ilimin da ya dauka bashi da wata alkiblar da zai ciyar da jihar Kano gaba,” a cewar Ganduje.

Sannan ya kara da cewa, “da shigar mu gwamnati ya fara sukar u a kan cewar mun kasha bangaren ilimi. Mutumin da bai yi wani karatun kirki ba ne ke sukar mai digiri uku (PhD) da Farfesa a kan cewar basu san yadda za su kawo cigaba a bangaren ilimi ba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel