Zaben Gwamna: An fara jigilar kayayyakin zabe a jihar Kano

Zaben Gwamna: An fara jigilar kayayyakin zabe a jihar Kano

A yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnoni da kuma na 'yan majalisun dokoki na jiha, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta fara tantance muhimman kayayyakin zabe domin jigila a jihar Kano.

Mun samu cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta fara rarraba muhimman kayayyakin zabe tare da jigila cikin kananan hukumomi 44 a jihar Kano yayin shirin gudanar da zaben gwamna da kuma na 'yan majalisun dokoki a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Zaben Gwamna: An fara jigilar kayayyakin zabe a jihar Kano
Zaben Gwamna: An fara jigilar kayayyakin zabe a jihar Kano
Asali: UGC

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wannan shiri ya biyo bayan tattara na'urar tantance masu kada kuri'u ta katin su na zabe da kuma takardun dangwala kuri'u a babban bankin Najeriya reshen jihar Kano a yau Laraba.

Shugaban hukumar INEC reshen yada bayanai da rahotanni, Mallam Garba Muhammad, shine ya bayar da shaidar wannan lamari yayin ganawar sa da manema labarai na jaridar The Punch ta hanyar wayar salula ta sadarwar zamani.

KARANTA KUMA: Masana sun shawarci Buhari kan cire tallafin man fetur

Mallam Muhammadu ya yi bayanin cewa, tuni hukumar ta kammala jigila gami da rarraba kananan kayayyakin zabe ta fuskar muhimmanci zuwa kananan hukumomi 44 da ke fadin Kanon Dabo.

Rahotanni kamar yadda shugaban hukumar ya bayyana, bayan kammala tantancewa tare da warware muhimman kayayyakin zabe, ana sa ran za a fara jigila tare da rarraba su cikin birnin Kano da kewanye a Yammacin yau na Laraba da Hausawa ke ma ta lakabi da Tabawa ranar samu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel