An fara: Kotu ta karbi korafin Atiku na duba kayan aikin zabe

An fara: Kotu ta karbi korafin Atiku na duba kayan aikin zabe

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa a yanzu haka kwamitin mutum uku da aka kafa na sauraron karar zaben Shugaban kasa wanda dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, ya shigar inda yake neman a binciki kayayyain zaben da aka yi amfani da su a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu.

Kwamitin mutum ukun wanda ya fara zama a ranar Laraba, 6 ga watan Maris ya samu jagorancin Justis Abdul Aboki, yayinda Justis Peter Ige da Emmanuel Agim suka kasance mambobi a kwamitin.

Mista Livy Ozoukwu (SAN) ne ke jagorantar tawagar masu karar amma Cif Cgris Uce (SAN), ne ke gabatarwa a madadin tawagar.

An fara: Kotu ta karbi korafin Atiku na duba kayan aikin zabe
An fara: Kotu ta karbi korafin Atiku na duba kayan aikin zabe
Asali: UGC

Kamar yadda aka sanya rai, wadanda ake karan Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ba su hallara ba sannan kuma lauyoyinsu basu wakilce su ba.

Idan za’a tuna Atiku Abubakar ya sha kayi a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasar Najeriya daya gudana a ranar 23 ga watan Satumba, inda Buhari yaba Atiku tazarar kuri’u miliyan hudu.

KU KARANTA KUMA: Zan zage damtsen aiki sosai a wannan karon - Buhari

Sai dai Atikun ya nuna rashin amincewarsa da sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta sanar, inda ya dauki alwashin kalulabantar sakamakon zaben a gaban kuliya manta sabo, har sai ya kwato hakkinsa daga wajen Buhari.

Atiku ya danganta rashin amimcewarsa da sakamakon ga yawan masu kada kuri’a da aka samu a jihohin dake yankin Arewa maso gabas, yankin da Buhari keda dimbin masoya da magoya baya da suka bashi mamakon kuri’u.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel