Da duminsa: Gwamna El-Rufai ya samu goyon bayan kungiyar matasan Arewa

Da duminsa: Gwamna El-Rufai ya samu goyon bayan kungiyar matasan Arewa

- Kungiyar matasan Arewa (AYF) ta goyi bayan takarar gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai

- Kungiyar AYF ta ce gwamna El-Rufai ya cancanci tazarce, musamman idan aka duba kokarinsa na ganin cewa an dakile matsalar tsaro a jihar Kaduna

- Kungiyar ta jinjinawa matasan Nigeria kan yadda suka nuna dattako a yayin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya

Kungiyar matasan Arewa (AYF) ta goyi bayan takarar gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, tana mai bayyana shi a matsayin wanda ya fi cancanta ya ci gaba da mulkin jihar.

Kungiyar AYF reshen jihar Kaduna, a cikin wata sanarwa daga hannun kodinetanta, Abba Ismail, ta yi kira ga matasa da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin zabar gwamnan jihar Nasir El-Rufai karkashin jam'iyyar APC.

Kungiyar AYF ya ce gwamna El-Rufai ya nuna cikar kamalarsa ta zama shugaba wanda ya zama wajibi a yaba masa, musamman kokarinsa na ganin cewa an dakile matsalar tsaro a jihar Kaduna.

KARANTA WANNAN: Zaben gwamnoni: Yadda takardun rubuta sakamakon zabe suka bace a Delta

Da duminsa: Gwamna El-Rufai ya samu goyon bayan kungiyar matasan Arewa
Da duminsa: Gwamna El-Rufai ya samu goyon bayan kungiyar matasan Arewa
Asali: UGC

Sanarwar ta ce: "Kungiyar AYF ta jinjinawa matasan Nigeria kan yadda suka nuna dattako a yayin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabreru da kuma fatan za su maimaita hakan a zaben gwamnonni da na 'yan majalisun dokoki da za a gudanar Asabar mai zuwa.

"A wannan gabar, muke kiran dukkanin mambobin kungiyar AYF da ke a kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna, da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin zaben Mallam Nasiru El-Rufai saboda irin ci gaban da ya kawo da kuma dakile matsalolin tsaro a jihar.

"Hakika ko a iya haka, gwamnan ya cancanci yabo da kwatantawa a matsayin misali na shugaba na gari da kuma sanin hanyoyin raba romon demokaradiyya a birni da kauyukan jihar Kaduna. Tabbas, El-Rufai ne wanda ya fi cancanta ya ci gaba da mulkin jihar."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel