Ta bayyana: Yan siyasa na kokarin sanya Bam ranar zaben gwamnoni - Janar Buratai

Ta bayyana: Yan siyasa na kokarin sanya Bam ranar zaben gwamnoni - Janar Buratai

Babban hafsan sojin Najeriya, Laftana Janar Tukur Buratai, a ranar Laraba, ya bayyana cewa hukumar sojin ta gano shirin da wasu yan siyasa ke yi domin tayar da hankali ranar zabe wanda ya hada da sanya bama-bamai.

Ya bayyana hakan ne yayi ganawarsa da kwamandoji, manyan hafoshi da diraktoci a hedkwatan soji dake birnin tarayya, Abuja.

Yace binciken leke asiri da aka gudanar na nuna cewa wasu yan siyasa suna shirye-shiryen hana zaman lafiya yayin zaben gwamnoni da yan majalisun dokokin jiha.

Yace: "Akwai alamun cewa suna shirin amfani da rikicin makiyaya da manoma, yan bangan siyasa da yan daba domin tayar da rikici wanda ya hada da tayar da bama-bamai."

"Wasu na shirin amfani da ma'aikatan abokan hamayyarsu, daukan makasa domin kashe mutane, amfani da kafafen yanar gizo domin yada jita-jita, maganganun batanci da labarun karya domin kawo rashin zaman lafiya."

"Kada mu sake mu bari su samu nasara. Ba zamu amince wadanda suka rantse sai sun kawo cikas zabenmu su samu nasara ba."

Ya kara da cewa wannan zaben na gwamnoni da ya majalisun jihohi na da matukar muhimmanci saboda ya fi shafan mutane kuma da yiwuwan a samu matsaloli daban-daban.

Yayi kira ga dukkan kwamandojinsa da suyi aiki tukuru tare da ma'aikatun gwamnati da sauran yan Najeriya wajen samun nasara a zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel