Masana sun shawarci Buhari kan cire tallafin man fetur

Masana sun shawarci Buhari kan cire tallafin man fetur

Kwararru daga kasashen ketare da kuma na nan gida Najeriya, sun yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari karin haske dangane cire tallafin man fetur yayin jagorancin kasar nan a karo na biyu domin habaka tattalin arziki.

Cibiyar kididdiga ta Agusto & Co Limited, ta shawarci shugaban kasa Buhari kan cire tallafin man fetur da kuma rage tsadar farashin kudin ruwa yayin yunkurin habaka tattalin arzikin kasar nan a mulkin sa karo na biyu.

Shafin jaridar The Punch ya ruwaito cewa, kwararrun masana bunkasar tattalin arziki sun shawarci zababben shugaban kasar Najeriya da ya sanya akida ta cire tallafin man fetur, rage tsadar farashin kudin ruwa cikin muhimman manufofi da tsarin sa na jagoranci a karo na biyu.

Masana sun shawarci Buhari kan cire tallafin man fetur
Masana sun shawarci Buhari kan cire tallafin man fetur
Asali: Twitter

Cibiyar kwararrun ta nemi shugaba Buhari da ya jajirce wajen samar da kudaden shiga yayin yunkurin sa na sauya shimfidar tsare-tsare na sauya fasalin yadaa gwamntai ke bad da dukiya wajen gudanar da al'amurranta.

KARANTA KUMA: Buhari ya taya Obasanjo murnar cika shekaru 82 a duniya

A cewar babbar cibiyar, dole gwamnatin shugaba Buhari ta zage dantse ta fuskar yarjewa 'yan kasuwa sanya hannayen jari wajen inganta ci gaban gine-ginen kasa ka ma daga filayen jiragen sama, layin dogo da kuma harkokin wutar lantarki.

Jagoran cibiyar tsantseni da bunkasar tattalin arziki na duniya, Charlie Robertson, cikin wani sako da ya aike zuwa Najeriya ta hanyar sadarwar zamani a yau Talata, ya ce dole Najeriya ta nunka farashin man fetur ko kuma tumfaya ingancin masana'antu domin kai wa zuwa tudun tsira ta fuskar habakar tattalin arziki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel