Zaben gwamnoni: Yadda takardun rubuta sakamakon zabe suka bace a Delta

Zaben gwamnoni: Yadda takardun rubuta sakamakon zabe suka bace a Delta

A yayin da ya rage saura kwanaki biyu a gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisun tarayya, an nemi takardun rubuta sakamakon zabe na kananan hukumomi guda hudu a jihar Delta an rasa.

Wata majiya daga hukumar, ta sanarwa Vanguard cewa, sun gano cewa babu takardun rubuta sakamakon zaben kananan hukumomin a lokacin da ake kan bin diddigin kayayyakin zaben a cikin babban bankin Nigeria CBN, reshen Asaba, a yammacin ranar Litinin.

A yayin da ya ke zargin wasu manyan jam'iyyun siyasa na shirin tafka magudin zabe ta hanyar hadin kai da hukumar INEC da jami'an tsaro a zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki, ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su kasance cikin shiri domin ganin cewa shirin magudin bai tabbata ba a jihar.

KARANTA WANNAN: Zaben 2019: INEC ta sallami wasu jami'an zabe a Borno, ta dauki wasu sabbi

Zaben gwamnoni: Yadda takardun rubuta sakamakon zabe suka bace a Delta
Zaben gwamnoni: Yadda takardun rubuta sakamakon zabe suka bace a Delta
Asali: Original

Majiyar ta yi ikirarin cewa akwai wani shiri da ake yi na tayar da kura a jihar domin cusa tsoro da dari-dari a zukatan al'ummar jihar da nufin hana masu kad'a kuri'a fitowa domin yin zabe a wasu kananan hukumomi da ke a mazabar Delta ta Kudu.

Duk wani yunkuri na jin ta bakin kwamishinan hukumar zabe na jihar, Dr Cyril Omorogbe domin karin bayani kan lamarin ya ci tura.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel