Yan bindiga sun tarwatsa gangamin kamfen din APC a Akwa-ibom

Yan bindiga sun tarwatsa gangamin kamfen din APC a Akwa-ibom

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba a yammacin ranar Talata, 5 ga watan Maris sun bude wuta a taron kamfe din jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hanyar Edet Apkan Avenue, Uyo da ke jihar Akwa Ibom.

Wasu da dama sun ji rauni a harin.

Wani dan acaba da ya shaidi faruwar lamarin yace ya ga mazaje uku sun fito daga mota kirar Toyota Hilux wacce aka ajiye a ketaren titi, inda ake gudanar da yakin neman zaben wacce aka fi sani da Nsima Ekere campaign ground.

Yace mutanen sun ketaro daga titin, suka tsaya a mashigin harabar inda ake gudanar da taron sannan suka bude wuta a harabar kafin suka tsere.

Yan bindiga sun tarwatsa gangamin kamfen din APC a Akwa-ibom
Yan bindiga sun tarwatsa gangamin kamfen din APC a Akwa-ibom
Asali: Depositphotos

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, wanda ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci inda lamarin ya auku, tare da shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole, da sauran jiga jigan APC don gangamin siyasa.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya san cewa yan Najeriya sun sha wuya matuka – Amaechi

Jam’iyyar APC ta bayyana jawabi akan lamari, har da hoton daya daga cikin wadanda suka ji rauni a asibiti.

Jam’iyyar APC ta zargi jamiyyar adawa (PDP) da kasancewa da hannu cikin harbe harben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel