Shugaban majalisar dattawa: Sanatocin APC sun mika ma Buhari wuka da nama

Shugaban majalisar dattawa: Sanatocin APC sun mika ma Buhari wuka da nama

Sanata mai wakiltar mazabar Delta ta tsakiya a jahar Delta, Sanata Ovie Omo-Agege na jam’iyyar APC ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai zabo Sanatan da zai jagoranci majalisar dattawa ta tara.

Legit.ng ta ruwaito Sanata ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da kamfanin dillancin labaru, NAN, a garin Warri na jahar Delta, inda yace shugaba Buhari da jam’iyyar APC ba zasu sake maimaita matsalar data faru a 2015 ba.

KU KARANTA: Buhari ya aika ma wata kasar Afirka tallafin naira miliyan 180.5 don gudanar da zabe

Shugaban majalisar dattawa: Sanatocin APC sun mika ma Buhari wuka da nama
Sanata Omo Agege
Asali: Depositphotos

“Duk wanda zai zama shugaban majalisar dattawa ta 9, dole ne ya kasance mutumin dake yin biyayya ga shugaban kasa, da jam’iyyar APC da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya, shugaban kasa ne zai jagoranci akalarmu wajen zaben shugaban majalisa, shi zai nuna mana wanda yake don yin aiki tare da shi.” Inji shi.

Jam’iyyar APC ce za ta samar da shugaban majalisar dattawa biyo bayan samun kujeru mafi yawa a majalisar a zaben Sanatoci daya gudana a ranar 23 ga watan Feburairu, sai dai Sanata Omo Agege ya musanta batun mika ma yankin kasarnan kujerar.

“Ina da tabbacin zamu samu majalisar dattawa da za tayi aiki hannu da hannu da shugaban kasa, bamu sake barin marasa kishin shugaban kasa, marasa kishin jam’iyya su sake mulkar majalisar, inda yakinin Buhari zai shiga tsundum cikin tsare tsaren zaben shugaban majalisa da sauran shuwagabannin.

“Ire irena da suka dawo majalisa da suka dace da wannan mukami muna da yawa, amma duk hukucin da shugaban kasa ya yanke zamu bi shi sau da kafa, muna matukar son ganin Buhari ya samu nasara, don haka bamu kaunar a sake samun irin matsalar da ta haifar da Saraki.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel