Zaben 2019: INEC ta sallami wasu jami'an zabe a Borno, ta dauki wasu sabbi

Zaben 2019: INEC ta sallami wasu jami'an zabe a Borno, ta dauki wasu sabbi

- INEC a jihar Borno ta sallami wasu jami'an zabe domin tabbatar da cewa ta gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisun tarayya cikin nasara a jihar

- Hukumar ta bayyana cewa wasu daga cikin jami'an zaben da aka sallama sun gaza yin amfani da na'urar tantance masu kad'a kuri'a, wanda ya jawo tsaiko a zaben

- INEC ta dauki jami'an zabe na wucin gadi guda 22,500 aiki domin isar da rumfunan zabe 3,932 da kuma akwatunan zabe 5,071 da mu ke da su a jihar Borno

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a jihar Borno ta sallami wasu jami'an zabe na wucin gadi tare da musanyasu da wasu sabbi domin tabbatar da cewa hukumar ta gudanar da zaben gwamnoni da na 'yan majalisun tarayya cikin nasara a jihar Borno.

Kwamishinan hukumar na jihar Borno, Alhaji Mohammed Ibrahim, ya bayyana hakan a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, a ranar Laraba, a garin Maiduguri.

Ya ce hukumar ta musanya jami'an tsaron saboda gazawarsu na gudanar da ayyukan da aka basu a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabreru.

KARANTA WANNAN: Daga karshe: Mun gano shirin APC na tafka magudi a zaben gwamna a jihar Filato - PDP

Zaben 2019: INEC ta sallami wasu jami'an zabe a Borno, ta dauki wasu sabbi
Zaben 2019: INEC ta sallami wasu jami'an zabe a Borno, ta dauki wasu sabbi
Asali: Twitter

Ibrahim ya bayyana cewa wasu daga cikin jami'an zaben da aka sallama sun gaza yin amfani da na'urar tantance masu kad'a kuri'a, wanda ya jawo tsaiko a zaben.

"Mun dauki jami'an zabe na wucin gadi guda 22,500 aiki domin isar da rumfunan zabe 3,932 da kuma akwatunan zabe 5,071 da mu ke da su a jihar Borno. Musanya jami'an zaben tuni ya kammala kuma muna da wasu jami'an a kasa. INEC ta shirya tsaf domin ganin ta gudanar da zabe cikin nasara," a cewarsa.

Ibrahim ya yi nuni da cewa an zabo jami'an zaben daga ma'aikatan gwamnatin tarayya, matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC), malaman jami'o'i da kuma sauran manyan makarantu na jihar.

Ya uma bayyana cewa hukumar ta gudanar da sabon horo ga jami'an zaben kan yadda za su gudana da ayyukansu kamar yadda ya dace.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel