Yan bindiga sun halaka yan achaba guda 2, sun yi awon gaba da baburansu

Yan bindiga sun halaka yan achaba guda 2, sun yi awon gaba da baburansu

Wasu gungun yan fashi da makami sun halaka yan achaba guda biyu a unguwar Badagry ta jahar Legas, sa’annan suka yi awon gaba da baburansu, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ya bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kisan farko ya faru ne da misalin karfe 11 na daren Lahadin data gabata, yayin da kisan dan achaba na biyu kuma ya auku da sanyin safiyar Litinin, da misalin karfe 6 na safe.

KU KARANTA: Buhari ya aika ma wata kasar Afirka tallafin naira miliyan 180.5 don gudanar da zabe

Majiyar ta kara da cewa kisan farko anyi shi ne a cikin unguwar Ibereko, yayin da kisa na biyu aka gudanar da shi a gidan man Atanda dake layin Topo, duk a cikin yankin Badagry.

“Kwantan bauna yan fashin suka yi ma dan achaban a daidai mahadar hanya ta Ibereko, nan take suka kasheshi, suka yi awon gaba da babur dinsa, haka nan suka sake yi ma gudan dan achaban a gidan man Atanda, tuni mun mika gawarwakinsu zuwa dakin ajiyan gawa na asibitin Badagry.” Inji shi.

Sai dai da majiyarmu ta tuntubi rundunar Yansandan jahar don jin ta bakinta, sai kaakakinta yace har zuwa lokacin tattara wannan rahoto basu samu labari daga ofishin Yansandan Badagry ba.

A wani labari kuma, rundunar Yansandan jahar Ogun sun samu nasarar kama wani matashi dan shekara 29, Owolabi Folorunso Adewale da ya halaka innarsa mai shekaru 99 a duniya, Ebunola Aroboto a gidanta dake layin Maraisa, cikin yankin Ago-Iwoye na jahar Ogun.

Owolabi ya bayyana cewa ya kashe Aroboto ne saboda yana zarginta da sa hannu cikin matsalolin da yake fama dasu a rayuwarsa, inda yace ta kware wajen aika masa da ayyukan asiri da tsafe tsafe don kada ya cigaba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel