Jefa rai cikin hatsari da sunan murnar siyasa abun kyama ne – Shehu Sani yayi gargadi

Jefa rai cikin hatsari da sunan murnar siyasa abun kyama ne – Shehu Sani yayi gargadi

Sanata Shehu Sani ya bayyana matsanancin bukukuwa da magoya bayan yan siyasa ke yi a fadin kasar a matsayin abun kyama kuma abun Allah wadai.

Sanatan mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasar, ya bayyana hakan ne a safiyar ranar Talata, 5 ga watan Maris bayan raoton mutuwar wani masoyin Buhari da ya sha ruwan kwata sakamakon nasarar shugaban kasar ya billo.

Sani a wani rubutu da ya wallafa a shafin twitter ya bayyana cewa shan guba ko kuma tukin ganganci don murnar nasarar siyasa ba shine hanyar da iyalan shugabannin siyasa ke bi don murna ba.

Dan majalisar ya kuma yi addu’a kan Allah ya ji kan masoyin Shugaban kasar da ya mutu.

A baya Legit.ng ta raoto cewa labarin mutuwar Bala Haruna, dan asalin jihar Bauchi wanda ya kasance babban masoyin Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi fice a ranar Talata, 5 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya san cewa yan Najeriya sun sha fama matuka – Amaechi

Haruna ya sha alwashin kwashe mintuna 10 a cikin kwata sannan ya sha ruwan kwatan idan har shugaba Buhari ya lashe zaben Shugaban kasa.

A take ranar da aka kaddamar da Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 23 ga watan Fabrairu da safiyar ranar Laraba, 27 ga watan Fabrairu, Haruna ya cika alkawarin da ya dauka kamar yadda ya shiga kwatan sannan ya sha ruwan dattin da ke ciki. An tattaro cewa ya mutu sakamakon fasewar hanji yan kwanaki bayan aikata hakan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel