Gwamnatin jihar Kano ta tallafawa mahauta 4983 da miliyan 99

Gwamnatin jihar Kano ta tallafawa mahauta 4983 da miliyan 99

Gwamnatin jihar Kano ta kashe N99 million kan tallafawa mahauta 4,983, cewar gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, a gidan gwamnanti ranar Talata, 5 ga watan Maris, 2019 inda yace an yi hakan ne domin karfafawa kasuwancinsu.

Ganduje ya kara da cewa an zabi mahautan ne daga kananan hukumomi 44 a fadin jihar Kano. kuma zuwa yanzu, gwamnatin jihar ta tallafawa akalla mutane 956,000 domin inganta tattalin arzikin jihar.

Ya ce ko wanne daga cikin mahautan 4,983 zai samu dubu ashirin N20,000 domin inganta sana'arsu.

Ya yi amfani da wannan dama wajen godiya ga mutan jihar da zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma dukkan yan majalisar dokokin tarayya karkashin jam'iyyar All Progressive Congress (APC).

Gwamnan ya yi kira ga mutan jihar su fito kwansu da kwarkwatansu ranar 9 ga watan Maris domin kada kuri'arsu na zaben gwamnoni da yan majalisar dokokin jiha.

A jawabinsa, kwamishanan ilimin jihar, Malam Muhammad Garba, ya ce gwamnan jihar ta samu nasarar cika dukkan alkawuranta da tayi yayin yakin neman zabe.

Kana ya yi kira ga wadanda suka samu wannan tallafi da suyi amfani da kudin wajen inganta kasuwancinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel