Buhari ya san cewa yan Najeriya sun sha wuya matuka – Amaechi

Buhari ya san cewa yan Najeriya sun sha wuya matuka – Amaechi

- Minstan sufuri, Rotimi Amaeci, ya ce shugaban kasa Buhari na sane da irin wahalar da yan Najeriya suka sha

- Amaechi ya jadadda cewa shugaban kasar zai bayar da hadin kai sosai wajen gudanar da ayyukan gwamnati saboda wannan dalili

- Daraktan kamfen din shugaban kasar ya mika godiya ga dukkanin yan Najeriya da suka sake zabar shugaban kasar a karo na biyu

Minstan sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ba da hadin kai Wajen gudanar da ayyukan gwamnati saboda “ya na da masaniya akan cewa yan Najeriya sun sha wuya.”

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Talata, 5 ga watan Maris, ministan ya gode wa yan Najeriya akan zabar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a da suka yi a lokacin zabe.

Buhari ya san cewa yan Najeriya sun sha wahala matuka – Amaechi
Buhari ya san cewa yan Najeriya sun sha wahala matuka – Amaechi
Asali: Depositphotos

Yace goyon bayan da jam’iyya mai ci ta samu a kudu ya karu sosai, inda ya kara da cewa akwai banbanci tsakanin sakamakon zaben yankin a 2015 da sakamakon zabe da aka gudanar kwanan nan.

Ministan sufurin yace babu wariyar masu zabe saboda mutane sun san cewa APC ce zata lashe zaben shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Dan Sule Lamido na shirin garzayawa kotu kan sakamakon zabe

Babban daraktan yace yana da muhimmanci a gabatar da addu’o’i ga wadanda suka rasa rayukansu a lokacin yakin neman zabe.

Har ila yau ya daura wa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) laifi wasu kalubale da kasar ke fuskanta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel