Buhari ya taya Obasanjo murnar cika shekaru 82 a duniya

Buhari ya taya Obasanjo murnar cika shekaru 82 a duniya

Bayan kirari na karamci gami da girmama, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya kwarara yabo da jinjina zuwa ga tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo yayin da ya cika shekaru 82 a doron kasa.

Yayin bayyana cancantar karamci da kuma lambar yabo, shugaban kasa Buhari ya jingina kyakkyawar akida ta ƙauna da kuma kishin kasar Najeriya da ta mamaye duk wata magudana da kafofin jini da ke zuciyar tsohon shugaban kasa.

Buhari ya taya Obasanjo murnar cika shekaru 82 a duniya
Buhari ya taya Obasanjo murnar cika shekaru 82 a duniya
Asali: UGC

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yiwa kasar nan gagarumar hidima ta fuskar dimokuradiyya da ba ta misali wajen inganta ci gaba da hadin kai.

Shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa, kawowa yanzu ba zai gushe ba wajen ci gaba da girmama tsohon shugaban kasa tare da sanya shi a mizani na mafi kololuwar karamci duk da sabani na akidu da ke tsakanin su a siyasance.

Jagoran na Najeriya ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da sa hannun mai magana da yawun sa, Mallam Garba Shehu da ya bayyana cewa, baya ga sabanin akidun siyasa da ke tsakanin su, Obasanjo ya cancanci duk wani uabo da jinjina sakamakon rawar da ya ke ci gaba da takawa wajen tabbatar da kwararar romon dimokuradiyya a kasar nan.

KARANTA KUMA: Dimokuradiyya ta gaji gwagwarmaya, ba zan daina caccakar Buhari ba - Obasanjo

Da yake mika sakon sa na taya murna ga tsohon shugaban kasa yayin cikar sa shekaru 82 a ban kasa, shugaba Buhari ya yi addu'a gami da fatan Mai Duka ya kara masa lafiya, ilimi, nisan kwana da kuma hikima wajen ci gaba da yiwa kasar Najeriya hidima da kuma al'ummar ta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel