Daga karshe: Mun gano shirin APC na tafka magudi a zaben gwamna a jihar Filato - PDP

Daga karshe: Mun gano shirin APC na tafka magudi a zaben gwamna a jihar Filato - PDP

- Jam'iyyar PDP a jihar Fillato ta zargi jam'iyyar APC da shirya wani makirci na tafka magudi a zaben jihar

- PDP ta yi ikirarin cewa APC na shirin amfani da jami'an tsaro domin hantara da kuma cin zarafin jama'a wanda zai iya cusa tsoro a zukatan al'ummar jihar

- Sai dai jam'iyyar ta bayyana zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da aka gudanar a matsayin babbar nasara ga jam'iyyar PDP a jihar Filato

A yayin da ya rage saura kwanaki ukku a yi zaben gwamnoni da na 'yan majalisun tarayya, wanda aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 9 ga watan Maris, jam'iyyar PDP a jihar Fillato ta zargi jam'iyyar APC da shirya wani makirci na tafka magudi a zaben jihar.

Chief Damishi Sango, shugaban jam'iyyar PDP a jihar, ya yi wannan zargin a wani taron manema labarai a garin Jos, da ya gudana a ranar Talata.

A cewar Sango, APC "na da shirye shirye a kasa" na yin amfani da jami'an tsaro da kuma sauran manyan masu ruwa da tsaki a harkokin zabe wajen tafka magudi a zaben gwamnan jihar, da nufin bata nasara.

KARANTA WANNAN: Dole acewa mijin iya baba: Har yau har gobe ni uban gidan Buhari ne - Obasanjo

Daga karshe: Mun gano shirin APC na tafka magudi a zaben gwamnoni na jihar Filato - PDP
Daga karshe: Mun gano shirin APC na tafka magudi a zaben gwamnoni na jihar Filato - PDP
Asali: Twitter

Sango ya yi ikirarin cewa jam'iyya mai mulki na shirin "amfani da jami'an tsaro domin hantara da kuma cin zarafin jama'a wanda zai iya cusa tsoro a zukatan al'ummar jihar a ranar zaben."

Ya kara da cewa suna zargin jam'iyyar APC da shirya makirci na yiwa jama'a barazana a manyan wuraren da PDP ke da tasiri, da kuma lalata kayan zabe tare da hana jami'an gudanar da zabe isa rumfunan zaben akan lokaci.

Sai dai Sango, ya bayyana zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabreru a matsayin "babbar nasara ga jam'iyyar PDP a jihar Filato", yana mai cewa jam'iyyar adawar ta samu nasara duk da irin magudin da aka tafka.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel