Hukumar EFCC ta kwace fasfot din surukin Atiku

Hukumar EFCC ta kwace fasfot din surukin Atiku

Hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta kwace fasfot din surukin tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, Abdullahi Babalele.

Ana bincikensa ne akan zargin satar kudi da yawansu ya kai kimanin Euro miliyan 150.

A jiya Talata, 5 ga watan Maris ne aka bayar da belin Babalele bayan ya sha tambayoyi na kimanin sa’o’i 72.

Ana bincikarsa ne tare da Mista Uyi Giwa-Osagie wani hadimin Atiku wanda hukumar ta fara kamawa.

Hukumar EFCC ta kwace fasfot din surukin Atiku
Hukumar EFCC ta kwace fasfot din surukin Atiku
Asali: Facebook

Sai dai har yanzu hukumar yaki da rashawar na rike da Uyi a daidai lokacin kawo wannan rahoton saboda “har yanzu ana kan bincike ne”.

KU KARANTA KUMA: Dan asalin jihar Bauchi ya mutu yan kwanaki kadan bayan yayi wanka da shan ruwan kwata don murnar nasarar Buhari

Wata majiya na EFCC wanda ta nemi a boye sunanta tace: “An bayar da belin surukin Atiku amma bias wasu shariuda da suka hada da kwace fasfot dinsa. Binciken da muke yi kan zargin da ake masa ya bukaci da mu hana duk wani zirga-zirgansa a kasar.

“Za a ci gaba akan haka har sai an kammala binciken da ake kan yi.”

Da yake amsa wata tambaya, majiyar ya kara da cewa: “Ana ci gaba da tsare Mista Uyi Giwa-Osagie wanda yake hadimin Atiku ne a Lagas. Ba zan iya cewa ga lokacin da za a ssake shi ba.

“Amma dai mun bayar da belin tsohon ministan ayyuka na musamman, Alh Tanimu Turaki.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel