Dimokuradiyya ta gaji gwagwarmaya, ba zan daina caccakar Buhari ba - Obasanjo

Dimokuradiyya ta gaji gwagwarmaya, ba zan daina caccakar Buhari ba - Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya yi karin haske dangane da dalilai da da suka sanya ya ke ci gaba da suka gami da caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma rashin 'yar ga Maciji tsakanin su a siyasance.

Obasanjo kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito ya bayyana cewa, gwagwarmaya tsakanin karya da gaskiya da tsarin shugabanci na dimokuradiyya ya yi tanadi shine babban dalilin da ya sanya ba zai gaza wajen suka gami da caccakar shugaban kasa Buhari.

Dattijon na kasa ya ke cewa, ba bu wani dalili na kyamar juna ko kuma kiyayya a tsakanin sa da shugaban kasa Buhari illa iyaka ci gaba da kwankwadar babban romo da tsarin mulki na dimokuradiyya ya yi tanadi.

Dimokuradiyya ta gaji gwagwarmaya, ba zan daina caccakar Buhari ba - Obasanjo
Dimokuradiyya ta gaji gwagwarmaya, ba zan daina caccakar Buhari ba - Obasanjo
Asali: UGC

Shafin jaridar The Punch ya ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa Obasanjo ya bayyana hakan a jiya Talata yayin bikin murnar cikar sa shekaru 82 a duniya da aka gudanar a babbar cibiyar nazari ta Olusegun Obasanjo Presidential Library da ke birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Obasanjo ya yi wannan furuci biyo bayan shawarar wani Basaraken gargajiya na kasar Yarbawa mai lakabin Alake of Egbaland, Oba Michael Gbadebo, da ya nemi ya kawo karshen suka da kuma caccakar shugaban kasa Buhari yayin cikar sa shekaru 82 a doron kasa.

KARANTA KUMA: PDP ta bukaci kotu ta tilastawa INEC sakin kayan zabe domin bincike

Yayin jaddada matsayar sa tare da watsi da shawarar Oba Gbadebo, Obasanjo ya kara da cewa, dimokuradiya ta yi tanadin bayyana ra'ayi tare da raddi ga duk wani shugaba da ya aikata ba daidai ba yayin rikon akalar sa ta jagoranci.

Tarihi ya tabbatar ta cewa, an haifi tsohon shugaban kasa a ranar 6 ga watan Maris na shekarar 1937, inda ya rike akalar jagorancin kasar nan har karo biyu na tsarin mulkin soji da kuma na farar hula wato dimokuradiyya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel