Abin da ya kamata ka sani game da tsohon Shugaba Obasanjo

Abin da ya kamata ka sani game da tsohon Shugaba Obasanjo

A jiya ne tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Mattew Aremu Obasanjo, ya cika shekaru 82 da haihuwa. An haifi Obasanjo ne a Ranar 5 ga Watan Maris a shekarar 1937. Mun kawo maku kadan daga cikin zarrar tsohon shugaban kasar.

Wani abu game da Cif Olusegun Obasanjo shi ne bai taba shan kasa a zaben da yake yi ba, kuma ya taba samun mulki a sama. Obasanjo ya kuma mulki Najeriya na shekaru 8 a jere, bayan ya shiga gidan yari, abin da babu wanda ya taba yi a tarihi.

KU KARANTA: Za mu tafi da kowa a wannan karon – inji Shugaba Buhari

Abin da ya kamata ka sani game da tsohon Shugaba Obasanjo
Obasanjo @ 82: Shugaban da ya fi kowa dadewa yana mulki
Asali: Facebook

1. Wanda ya fara yin mulki sau 2

Olusegun Obasanjo ya bar tarihi inda ya zama shugaban farko da yayi mulki a lokacin soji da kuma lokacin farar hula a Najeriya. Obasanjo ya mulki Najeriya bayan mutuwar Janar Murtala Muhammad da kuma 1999 zuwa 2007. Obasanjo ya kuma mika mulki ga wanda yake so a Jam'iyyar PDP.

2. Mikawa farar hula mulki a Afrika

A Nahiyar yammacin Afrika, kusan Olusegun Obasanjo ne shugaba na mulkin soja na farko da ya mika mulki zuwa ga farar hula a Najeriya. Obasanjo ya cika alkawarin da gwamnatin Murtala Muhammad ta dauka na yin zabe a 1979 inda Shehu Shagari ya doke sauran 'yan takara 4 a zaben kasar.

3. Tazarce a kan karagar mulki

A 1999 ne Olusegun Obasanjo ya sake darewa kan mulki a karkashin PDP bayan ya doke Olu Falae na AD. A 2003 kuma Obasanjo ya doke wasu ‘yan takara ya samu zarcewa kan mulki. Wannan ya sa ya zama wanda ya fara kammala wa’adin sa a Najeriya. A baya an hambarar da Gwamnatocin Shehu Shagari da Abubakar Balewa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel