NNPC zata gina tashan wutan lantarki a Abuja, Kaduna da Kano

NNPC zata gina tashan wutan lantarki a Abuja, Kaduna da Kano

Kamfanin man feturin Najeriya NNPC ta laburta cewa ta shirya tsaf domin gina tashan wutan lantarki a birnin tarayya Abuja, jihar Kani da Kaduna wanda zai kara karfin wutan Migawat 4000 domin amfanar al'ummar Najeriya.

Kana zata gina masana'antar hada takin zamani a garin Brass, jihar Bayelsa, kudancin Najeriya.

Shugaban kwamitin kamfanin NNPC, kan iskar Gas da wutan lantarki, Mr Isiaka AbdulRazaq, ya bayyana hakan ne a ganawarsu a ofishin NNPC dake Abuja.

Mista AbdulRazaq yace an kafa sashen wutan lantarki GPIC daga NNPC ne saboda habaka rayuwar Najeriya, inda yace idan aka kammala wadannan tashohin wutan lantarkin, kananan yan kasuwa sa ke wuraren zasu ji dadi.

Yace: "GPIC kamfani ce wacce NNPC ta kafa domin ganin yadda zata habaka arzikin iskar gas na kasar nan da kuma samar da kudi. Kamfanin zata mayar da hankali wajen inganta tashohin wutar lantarki, masana'antun takin zamani."

Ya kara da cewa wannan kamfani zata taimaka wajen inganta biyan harajo da samawa Najeriya kudin shiga.

Ya ce masana'antar hada takin da za'a gina a Brass, jihar Bayelsa zai habaka aikin noma a yankin kudu maso kudanci da sauran yankunan Najeriya.

KU KARANTA: Kujerar shugaban majalisar dattawa: Tsaffin gwamnoni na shirya tuggu

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel