Za mu tsaurara tsaro a zabe mai zuwa - Hukumomin tsaro

Za mu tsaurara tsaro a zabe mai zuwa - Hukumomin tsaro

-Duk wanda ya saba dokokin zabe, to, ya kuka da kansa

-Za mu rubanya a kan tsaron da muka bayar a zaben shugaban kasa

-Kowane dan Nijeriya da ya isa zabe ya fito ya kada kuri'a ga dan takarar da ya ke so ba tare da fargaba ba

A jiya Talata, shugabannin hukumomin tsaro na kasa sun bayyana cewa sun kammala dukkan shirye-shiryen da ya kamata na tunkarar zaben gwamnoni da 'yan majalisun dokoki a fadin Nijeriya

Shugabannin tsaro sun yi jan kunne ga masu niyyar tayar da hankula a zaben da su sauya tunani ko kuma su kuka da kansu.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, za ta  gudanar da zabukan gwamnoni da 'yan majalisunsu a jihohi 29 na kasar nan a ranar Asabar 9 ga watan Maris.

KU KARANTA: Mun cafke mutum 323, jami'anmu 2 sun rasa ransu a zaben da ya gabata - Sufeton 'yan sanda

Hukumomin tsaron sun bayyana shirinsu ne a jiya a yayin wata ganawa da suka yi da shugaba Buhari a fadar gwamnatin tarayya da ke a Aso Villa Abuja.

Ganawar a tsawon awanni biyu a samu halartar Babban hafsan hafsoshin tsaro na kasa, Janar Gabriel Olonisakin, Hafsan sojojin kasa, Lafanal Janar Tukur Yusuf Buratai, Hafsan sojojin ruwa, Riya Admiral Ibok Ekwe Ibas da Hafsan sojojin sama, Eya Mashal Abubakar Sadique.

Sauran sun hada da: Mai bada shawara kan harkokin tsaro, Babagana Munguno, Minisatan tsaro, Mansur Dan Ali, Ministan cikin gida, Janar Abdurrahman Dambazau mai ritaya, Babban daraktan hukumar fikira, Ahmad Abubakar, Sufeto janar na 'yan sanda, Muhammad Adamu da daraktan jami'an tsaron fararen kaya, Yusuf Magaji Bichi.

KU KARANTA: Assha: An kama mataimakin majalisar dokokin jihar Nasawara da matar aure a otal

Bayan taron na sirri, Babban sufeton 'yan sanda, Muhammad Adamu ya yi wa manema labarai bayanin da taron ya kunsa a takaice, inda ya ce za a kara tsaro sama da wanda aka bayar a zaben shugaban kasa da 'yan majalisar tarayya.

"Muna sane da cewa an kammala zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya cikin nasara da kwanciyar hankali da lumana. Muna taya 'yan Nijeriya samun nasarar zabe cikin lumana, kuma mun kammala shiri tsaf na tunkarar zabe mai zuwa na gwamnoni da 'yan majalisar jiha a ranar Asabar mai zuwa.

"Muna masu kira da 'yan Nijeriya da su fito su kada kuri'unsu ga wadanda suke so domin muna dada inganta tsaro sama da yadda muka bayar a zaben da ya gabata." inji Sufeton 'yan sandan.

Sufeton 'yan sandan ya kara da cewa sun yanke shawarar zafafa hukunci ga duk wanda aka kama da nufin kawo rudani a lokacin zaben.

KU KARANTA: Wata jam'iyya ta maka Shugaba Buhari da Atiku a gaban kuliya

"Muna kuma bayar da shawara ga wadanda ke da niyyar kawo rikici a lokacin zaben da su sake tunani. An samu 'yan matsaloli nan da can a lokacin zaben shugaban kasa, a saboda haka ne ma muka zauna muka sake nazarin yadda za mu shawo kan wadancan matsaloli da muka samu a baya.

"Ba za mu yarda da dabanci ba, ba za mu yarda da satar akwatu ba, ba za mu yarda da duk wani shiri na kawo hargitsi a wajen zabe ba. Mu jami'an tsaro mun yake hukuncin aiwatar da hukunci mai radadi ga duk wanda muka samu da kokarin kawo hargitsi kowane iri ne.

"A saboda haka ne ma muke kira ga al'umma da mu girmama dokokin zabe," inji Sufeto janar na 'yan sandan Nijeriyan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel