EFCC na kokarin karbe hujjojin Atiku na zuwa Kotu - CUPP

EFCC na kokarin karbe hujjojin Atiku na zuwa Kotu - CUPP

Gamayyar kungiyar Coalition of United Political Parties (CUPP) ta zargi hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) da tursasa mataimakin daraktan kungiyar yakin neman zaben dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), da ya mika shaidar da Atiku Abubakar yake yunkurin yin amfani da su a kotu.

Atiku ya kaddamar da lauyoyi yan kwanaki da suka gabata don kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranan 23 ga watan Fabrairu inda hukumar INEC ta bayyana dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben.

EFCC na kokarin karbe hujjojin Atiku na zuwa Kotu - CUPP
EFCC na kokarin karbe hujjojin Atiku na zuwa Kotu - CUPP
Asali: Twitter

Sai dai hukumar EFCC a ranan Litinin da ya gabata ne ta kama Turaki, tsohon ministan ayyuka na musamman wanda jam’iyyar PDP tace yana tare da jerin shaidu da Atiku ke yinkurin gabatarwa a matsayin shaidunsa sannan kuma da zargin cewa hukumar EFCC na kokarin tursasa Turaki don ya gabatar da jerin shaidu akan jam’iyyar APC.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai tafi da kowa a wannan karon – Inji Amaechi

A wani jawabi a ranar Talata a Abuja, kakakin kungiyar CUPP, Ikenga Ugochinyere yace, “EFCC na so ne ta kwace takardu da shaidu da Atiku zai gabatar akan Buhari don janye hankula daga rubutacciyar kara da bata wassu shaida dake nuna magudi a zaben da aka gudanar wadanda Turaki ya mallaka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel