EFCC za ta hada gwiwa da FRSC, NSCDC da Immigration kan yakar cinikin kuri'u (Hotuna)

EFCC za ta hada gwiwa da FRSC, NSCDC da Immigration kan yakar cinikin kuri'u (Hotuna)

A ranar 5 ga watan Maris na 2019 ne ofishin Hukumar Yaki da masu yiwa arzikin kasa zagon kasa EFCC reshen garin Ibadan ta kulla alakar hadin gwiwa da wasu hukumomin tsaro domin hana saye sa sayar da kuri'u a zaben gwamna da 'yan majalisun jiha da za a gudanar a jihar ranar Asabar.

Wannan ya biyo bayan wata ziyarar ban girma da shugaban hukumar na Ibadan, Mr Friday Ebelo ya kai zuwa ofisoshin hukumomin tsaron a ranar Talata kamar yadda EFCC ta bayanna a shafinta na Facebook.

Mr Ebelo ya ziyarci ofisoshin Hukumar Kiyaye Haddura na kasa FRSC, Hukumar Tsaro na NSCDC da Hukumar Kula da Fita da Shigen al'umma wato Immigration domin ya isar da sakon shugbann riko na EFCC, Mr Ibrahim Magu na hana cinikin kuri'a saboda a samu tsaftattacen zabe.

DUBA WANNAN: Tarihi: Kyawawan hotunan shugabannin Najeriya 5 da matan su

A yayin da suka karbi bakuncinsa, Mrs Cecelia Alao (Babban Kwamandan FRSC); Dr John Adewoye (Shugaban NSCDC na jihar Oyo) da Mr Sale Azare Abdullahi (Comptroller na Immigration) sun yabbawa namijin kokarin na EFCC kuma sunyi kira da sauran hukumomin tsaro su hada hannu da EFCC domin yaki da masu aikata almundaha da kudi da rashawa.

Ga hotunan yadda taron na shugaban EFCC da shugabanin hukumomin tsaron ya kasance a kasa:

Hana cinikin kuri'u: EFCC za tayi hadin gwiwa da FRSC, NSCDC da Immigration
Mr Friday Ebelo na EFCC da Mr Sale Azare Abdullahi na Hukumar Kula da Shige da Fice (Immigration)
Asali: Facebook

Hana cinikin kuri'u: EFCC za tayi hadin gwiwa da FRSC, NSCDC da Immigration
Mr Firday Ebelo na EFCC da Mrs Cecelia Alao na Hukumar Kiyaye Haddura na Kasa (FRSC)
Asali: Facebook

Hana cinikin kuri'u: EFCC za tayi hadin gwiwa da FRSC, NSCDC da Immigration
Mr Friday Ebelo na EFCC tare da Dr John Adewoye na Hukumar Tsaro ta NSCDC reshen jihar Oyo
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tarihi: Kyawawan hotunan shugabannin Najeriya 5 da matan su

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel