Kujerar shugaban majalisar dattawa: Tsaffin gwamnoni na shirya tuggu

Kujerar shugaban majalisar dattawa: Tsaffin gwamnoni na shirya tuggu

Tsofin gwamnonin Najeriya da suka samu nasarar cin kujeran Sanata suna shirga tuggu kan wadanda zasu zama shugabannin majalisar dokokin tarayya a zaben cikin gidan da za'a gudanar a watan Yuni.

An tattaro cewa tsaffin gwamnonin na shirin amfani da karfinsu wajen tilasta sauran yan majalisan zaben wanda zai zama shugaban majalisar dattawa.

Saraki, wanda ya ke shugaban majalisar ya sha kasa a zaben kujerara majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Kwara ta tsakiya na ranar 23 ga Febrairu. Ya fadi warwas a hannun dan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Yahaya Ibrahim Oloriegbe.

Wannan shine karo na farko da Saraki zai taba faduwa a zabe musamman a jihar Kwara.

Majiyar Legit ta bayyana cewa wasu tsofin gwamnoni suna ganawa a Abuja domin shirya wannan tuggu.

Anyi daya daga cikin ganawar ranar Lahadin da ya gabata a unguwar Asokoro dake birnin tarayya, gidan daya daga cikin gwamnonin.

KU KARANTA: NNPC zata gina tashan wutan lantarki a Abuja, Kaduna da Kano

A yanzu haka, tsofin gwamnoni 16 zasu shiga majalisar dattawa.

Goma daga cikinsu manya sanatoci ne saboda imma sun kasance tsafin yan majalisar wakilai ko majalisar dattawa. Sauran shidan sabbin shiga majalisa ne.

Kasancewa babban sanata na iya baiwa daya cikin goman zama shugaban majalisar.

Gwamnonin sune: Chimaroke Nnamani (Enugu); Ibrahim Shettima; Tanko Al Makura; Ibrahim Gaidam; Ibrahim Shakarau; Ibikunle Amosun; Rochas Okorocha; Gabriel Suswam da Abdullahi Adamu.

Sauran sune Mohammed Danjuma Goje; Orji Uzor Kalu, Theodore Orji; Kabiru Gaya, Aliyu Wamakko, Abdulaziz Yari, Adamu Aliero.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel