‘Dan takarar Jam’iyyar NRM ya kai APC da PDP kara Kotu saboda kudin kamfe

‘Dan takarar Jam’iyyar NRM ya kai APC da PDP kara Kotu saboda kudin kamfe

Labari ya kawo gare mu cewa ‘dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar NRM a zaben 2019, Usman Ibrahim Alhaji, ya shigar da kara a kan shugaban kasa Buhari da Atiku Abubakar na PDP.

‘Dan takarar Jam’iyyar NRM ya kai APC da PDP kara Kotu saboda kudin kamfe
Jam’iyyar NRM na so a soke takarar da APC da PDP su kayi
Asali: Facebook

Usman Ibrahim Alhaji na jam’iyyar adawa ta NRM yana korafin cewa shugaba Muhammadu Buhari da kuma babban abokin hamayyar sa watau Atiku Abubakar sun kashe kudin da ya wuce ka’ida wajen yakin neman zaben bana.

Alhaji Usman Ibrahim ya fadawa babban kotun tarayya da ke Abuja cewa a soke takarar da Muhammadu Buhari na APC da kuma Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, su kayi a zaben da ya gabata saboda sabawa doka.

KU KARANTA: An fadawa Atiku ya hakura da zuwa Kotu kan sakamakon zaben 2019

Lauyan ‘Dan takarar na shugaban kasa mai suna Ezekiel Ofor, yace kudin da manyan ‘yan takarar su ka batar a zaben shugaban kasa, ya haura abin da dokar zabe ta tanada wajen kamfe. Yanzu dai an fara sauraron wannan kara a Abuja.

A dokar kasa, bai halatta a kashe fiye da Naira Biliyan guda wajen yakin neman zaben shugaban kasa ba. Alhaji Usman Ibrahim, yana ganin cewa abin da PDP da APC su ka kashe a wajen yawon kamfe, duk ya haura Naira Biliyan guda.

Lauyan mai karar yake cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, wanda yayi takara a APC ya rika kashe dukiyar gwamnati wajen kamfe da sunan wani tsari na Trader Moni. Yanzu dai Alkali Ahmed Muhammad ya daga karar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel