Shugaba Buhari zai tafi da kowa a wannan karon – Inji Amaechi

Shugaba Buhari zai tafi da kowa a wannan karon – Inji Amaechi

Daily Trust ta rahaoto cewa Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa Buhari a jam’iyyar APC watau Rotimi Amaechi ya bayyana cewa gwamnatin su za ta tafi da kowa wannan mulkin.

Shugaba Buhari zai tafi da kowa a wannan karon – Inji Amaechi
APC tace Buhari ba zai manta da kowa ba a mulkin sa na karshe
Asali: UGC

Rotimi Amaechi yayi wannan bayani ne jiya Talata, lokacin da ya zanta da manema labarai a babban ofishin yakin neman zaben APC da ke cikin babban birnin tarayya Abuja. Amaechi ya kuma godewa mutanen da su ka zabi APC.

Ministan kasar ya bayyana cewa wannan karo, gwamnatin Buhari za ta soma aiki ne babu wata-wata, ba tare da bata lokaci ba. Rotimi Amaechi, yace jama’a sun tagayyara don haka, tun ranar gini, ran zane, domin abubuwa su yi kyau.

KU KARANTA: Yadda Saraki ya rasa kujerar sa a hannun Jam’iyyar APC a Kwara

Sarkin yakin na neman zaben shugaban kasa Buhari yake cewa za su yi kokarin ba marada kunya a shekaru 4 masu zuwa, kuma gwamnatin da za a kafa za ta janyo kowa a jika, sannan ayi wa mutanen kasar nan ayyukan da za su ji dadi.

Amaechi yace yanzu an gama kamfe don haka abin da ke gaban su shi ne yadda za a inganta tattalin arziki da kuma habaka sha’anin tsaro, wanda sai an samu zaman lafiya ne kowace kasa za ta iiya cigaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

https://youtu.be/4bu080k1o9w

Asali: Legit.ng

Online view pixel