Buhari ya aika ma wata kasar Afirka tallafin naira miliyan 180.5 don gudanar da zabe

Buhari ya aika ma wata kasar Afirka tallafin naira miliyan 180.5 don gudanar da zabe

A kokarinsa na cigaba da tabbatar da alakar diflomasiyya dake tsakanin kasashen biyu, shugaban kassar Najeriya, Muhammadu Buhari ya aika ma gwamnatin kasar Guinea Bissau tallafin kudi dala dubu dari biyar domin su samu damar shirya zabe a kasar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama ne Buhari ya aika da wadannan makudan kudade da sukayi daidai da naira miliyan dari da tamanin da dubu dari biyar (N180,500,000).

KU KARANTA: Sarakunan gargajiya sun kai ma Buhari gaisuwar jinjina da ban girma a Villa

Shugaba Buhari ya bada wannan tallafi ga kasar Guninea Bissau ne don ta samu damar gudanar da zaben yan majalisun dokokin kasar da ta shirya gudanarwa a ranar Lahadi, 10, ga watan Maris na shekarar 2019.

Kaakakin Minista Onyeama, Saeah Sand ace ta tabbatar da haka cikin wata sanarwa data fitar a ranar Talata, 5 ga watan Maris a babban birnin tarayya Abuja, inda tace ministan ya samu rakiyar shugaban kungiyar kasashen yammacin Afirka, Jean Calude Brou.

Ministan ya kara da cewa sun samu ganawa da shugaban kasar Guninea Bissau din, Joe Mari Vaza tare da shugaban kasar Guinea Conakry, Alpha Conde, inda shugaba Vaza ya bashi wata wasika dake kunshe da sakon taya murnar lashe zabe don ya mikata ga Buhari.

Haka zalika ministan a yace gwamnatin Najeriya ta baiwa kasar Guninea Bissau taimakon motocin aiki guda bakwai, da kuma kayayyakin zabe guda dari uku da hamsin, kuma ana sa ran gudanar da zaben shugaban kasa anan gaba kadan.

Daga karshe Onyeama ya tabbatar ma firai ministan kasar, Aristedes Gomes cewa zasu warware duk wasu kalubale da ka iya zama barazana game da gudanar da zaben, domin a baiwa yan kasa damar zaben yan majalisunsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel