Mu na taya Buhari murna kuma mu na kira ga Atiku ya zo a hada kai - NDFVF

Mu na taya Buhari murna kuma mu na kira ga Atiku ya zo a hada kai - NDFVF

Labari ya zo gare mu cewa wata fitacciyar kungiya a Neja-Delta tayi kira ga ‘dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar, da ya fasa shiga kotu a game da sakamakon zaben shugaban kasa.

Mu na taya Buhari murna kuma mu na kira ga Atiku ya zo a hada kai - NDFVF
Ana cigaba da rokon Atiku ya amince da sakamakon zaben 2019
Asali: UGC

Kungiyar Niger Delta Freedom Volunteer Force, NDFVF, tayi kira na musamman ga Atiku Abubakar ya hada-kai da shugaba Muhammadu Buhari domin ganin Najeriya ta cigaba. Atiku dai yana ganin cewa an murde masa zabe ne.

Wannan kungiya da ke kudancin Najeriya ta fadawa babban Abokin hamayyar na shugaba Buhari da ya rungumi kaddara a zaben 2019 da ya gabata. Kungiyar ta kuma yi kira ga daukacin mutanen kudu da su yadda da sakamakon zaben.

KU KARANTA: 2019: Mu hadu a gaban Alkali- Buhari ya fadawa Atiku

Shugaban wannan kungiya watau Harry Lawson da kuma Sakataren ta na kasa mai suna Preye Wilson su ne su ka bayyana wannan a wani jawabi da su ka fitar a Garin Fatakwal da ke cikin jihar Ribas, bayan PDP ta fara shirin zuwa kotu.

Babbar kungiyar ta ‘Yan Neja-Delta ta taya shugaba Muhammadu Buhari murnar sake lashe zaben Najeriya, tana kuma mai kira ga Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, ya zo a hada-kai wajen tafitar da kasar zuwa ga tudun-mun-tsira.

Kamar yadda mu ka ji, wannan kungiya ta zargi gwamnan jihar Nyesom Wike da kawowa Atiku Abubakar matsala a zaben da aka yi. NDFVF tace akwai laifin jiga-jigan PDP wajen nasarar APC a zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel