2019: Mun kagara mu hadu da Atiku a gaban Alkali inji APC

2019: Mun kagara mu hadu da Atiku a gaban Alkali inji APC

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a jam’iyyar APC ta fito tayi magana game da shirin da Atiku Abubakar yake yi na zuwa kotu bayan ya kashi a zaben da aka yi kwanaki.

2019: Mun kagara mu hadu da Atiku a gaban Alkali inji APC
Jam’iyyar APC tace babu matsala don Atiku ya tafi Kotu
Asali: Twitter

Kwamitin zaben na cewa babban Abokin hamayyar na shugaba Muhammadu Buhari watau Alhaji Atiku Abubakar. yana da damar zuwa kotu kamar kowa domin ayi masa adalci na karbo hakkin sa da yake tunani.an tauye masa.

Kakakin wannan kwamiti watau Festus Keyamo ya fitar da jawabi inda yace jam’iyyar APC ta shirya shiga kotu da Atiku. Keyamo yace ba su da niyyar hana ‘dan takarar na babban jam’iyyar adawar PDP neman hakkin sa a kotu.

KU KARANTA: Yadda aka murde zaben 2019 domin a tika PDP da kasa

Festus Keyamo mai magana a madadin jirgin yakin tazarcen na Buhari yace matsayar su shi ne, sun kagara Atiku ya maka su gaban Alkali. Keyamo ya nesanta kan su da kiran da wasu ke yi na hana Atiku kai kara a gaban kotu.

Keyamo yace hakan ne abin da ya dace kuma bai kamata wani ya hana Atiku daukar wannan mataki na shari’a ba. Lauyan yace yunkurin hana ‘dan takaran na PDP zuwa gaban kuliya yana iya jefa kasar cikin wani mawuyacin hali.

Jam’iyyar APC mai mulki tace idan har aka shiga kotu, za ta sake nunawa Duniya yadda ‘dan takarar na ta ya doke Alhaji Atiku Abubakar cikin ruwan-sanyi kamar yadda masu kula da zaben kasar su ka tabbatar a makonnin baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel