Bayan wuya akwai nasara: Kwararren Lauya ya karfafawa Atiku gwuiwar neman hakkin sa a kotu

Bayan wuya akwai nasara: Kwararren Lauya ya karfafawa Atiku gwuiwar neman hakkin sa a kotu

Daya daga cikin kwararrun lauyoyin nan a Najeriya kuma mai rajin kare hakkin bil'adama watau Femi Falana (SAN) a ranar Talata ya karfafawa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaben da ya gabata, Alhaji Atiku Abubakar gwuiwa game da zuwan sa kotu.

Babban Lauyan dai yace yana goyon bayan dan takarar yaje yabi kadin sa a kotu musamman ma tunda yana ganin kamar an zaluncewa ne duk da dai ya san akwai kalubalen shari'a mai girma da zai hadu da shi a katun.

Bayan wuya akwai nasara: Kwararren Lauya ya karfafawa Atiku gwuiwar neman hakkin sa a kotu
Bayan wuya akwai nasara: Kwararren Lauya ya karfafawa Atiku gwuiwar neman hakkin sa a kotu
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Jerin malaman addini 5 da suka kunyata tare da Atiku a zaben 2019

Haka ma dai Femi Falana a cikin wata takardar manema labarai da ya fitar, yace maganar da wasu keyi na neman su sa baki kar Atiku da jam'iyyar ta PDP su je kotu sam bai dace ba domin shi kan sa shugaba Buhari ya je kotu a zabukan shekarun 2003, 2007 da 2011.

Daga nan ne kuma sai ya shawarci hukumar INEC da kuma gwamnatin APC mai ci da su maida hankali wajen kawo gyare-gyaren da za su kara tsaftace zabukan da za'a rika gudanarwa a kasar tare da gyara kura-kuran da suka fito fili.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel