Kiran ruwa: Dan Allah kuyi hakuri, sarki gargajiya a Rivers ya roki hukumar Soji kan kisan Sojoji biyu a garin

Kiran ruwa: Dan Allah kuyi hakuri, sarki gargajiya a Rivers ya roki hukumar Soji kan kisan Sojoji biyu a garin

Wani sarkin gargajiya a jihar Rivers, Orubibiye Opuda VI of Abonnema, Alabo Tonye Douglas, a karamar hukumar Akuku-Toru na jihar Ribas ya kawo kukansa kan yadda akalla mazauna garin Abonnema 5000 suka gudu daga mulansu dare daya.

Mazauna Abonnema sun fara arcewa daga garin ne saboda tsoron martanin da hukumar soji za tayi bayan hallaka jami'anta biyu a garin.

Sarkin garin yana mai mika kokon bararsa ga hukumar sojin Najeriya kan suyi hakuri su yafewa al'ummarsa.

Douglas wanda tsohon minista ne yayi magana a birnin Fatakwal inda ya baiwa hukumar soji da gwamnatin tarayya hakuri kan kisa sojojin da akayi ba gaira ba dalili a kwanakin baya.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi, manyan sarakunan gargajiya, sun kaiwa Buhari ziyara

Yace: "A garin Abonnema, an shigo da yan daba da yawa, hakan ya sanya rayuwar sojojin cikin hadari. Muna rokon Soji suyi hakuri. Wannan abin da ya faru ya tayar da hankulan jama'a. Muna kiransu su tsaya amma suna guduwa domin tsoron abinda soji zasuyi."

Mun kawo rahoton cewa mutane da dama su na ficewa daga cikin Kauyen Abonnema da ke cikin karamar hukumar Akuku Toru a jihar Ribas bayan an kashe wasu sojojin Najeriya har 2 a daren Ranar Asabar dinnan da ta gabata.

Omoni Nnamdi, wanda shi ne kakakin ‘yan sanda na jihar Ribas, ya bayyanawa manema labarai cewa mutane da dama su na tserewa daga cikin karkarar Abonnema, tun da aka kashe wasu Dakarun sojoji a 'yan kwanakin nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel