Sarakunan gargajiya sun ziyarci Buhari domin taya shi murna, hotuna

Sarakunan gargajiya sun ziyarci Buhari domin taya shi murna, hotuna

A cigaba da karbar bakuncin kungiyoyi da manyan 'yan siyasa da ke taya shi murnar sake lashe zaben kujerar shugaban kasa a karo na biyu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin manyan sarakuna gargajiya daga arewa da kudancin Najeriya.

Sarakunan gargajiya sun ziyarci Buhari domin taya shi murna, hotuna
Sarakunan gargajiya sun ziyarci Buhari domin taya shi murna
Asali: Facebook

Ko a daren jiya, Litinin, sai da shugaba Buhari ya shirya wa shugabannin kwamitin yakin neman zaben sa (PCC) liyafar karrama wa da godiya.

A yayin hutun karshen mako ne shugaba Buhari ya halarci wata liyafar taya shi murna da kwamitin yakin neman zaben sa na bangaren mata da matasa ya shirya domi taya shi murnar lashe zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabarairu.

DUBA WANNAN: Jam’iyyu 32 da ‘yan takara 20 sun goyi bayan PDP domin kayar da gwamna Abubakar

Da duku-dukun safiyar ranar Laraba, 27 ga watan Fabarairu, ne INEC ta bayyana cewar shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben kujerar shugaban kasa.

Da ya ke sanar da sakamakon zaben, Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban INEC, ya ce Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 15,191,847 da su ka bashi nasara a kan abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar, na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 11,255,978.

A wani jawabi da ya fitar bayan shugaban INEC ya bayyana sakamako, Atiku y ace akwai alamun tambaya a kan sakamakon zaben tare da ikirarin cewar zai kalubalance shi a kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel