PDP ta bukaci kotu ta tilastawa INEC sakin kayan zabe domin bincike

PDP ta bukaci kotu ta tilastawa INEC sakin kayan zabe domin bincike

A yayin da Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ke ci gaba da bayyana rashin aminci tare da kalubalantar sakamakon babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019, a halin yanzu ya sake shigar da wani sabon korafi gaban kuliya.

'Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya nemi kotun karbar korafe-korafen zabe da ta tilastawa hukumar zabe ta kasa sakin muhimman kayayyakin da aka ribata wajen gudanar da babban zabe domin aiwatar da bincike.

PDP ta bukaci kotu ta tilastawa INEC sakin kayan zabe domin bincike
PDP ta bukaci kotu ta tilastawa INEC sakin kayan zabe domin bincike
Asali: Twitter

Jam'iyyar PDP da sanadin Lauyan ta, Cif Chris Uche (SAN), ta mika kokon barar ta a reshen kotun mai karbar korafe-korafen zaben shugaban kasa da ke garin Abuja da ta kasance wani rukuni na babbar kotun daukaka kara ta Najeriya.

Jam'iyyar PDP tare da dan takarar ta na kujerar shugaban kasa na neman samun damar gudanar da binciken diddigi kan wasu muhimman ababe na kayayyakin da ak ribata wajen gudanar da zabe da suka hadar da takardun kada kuri'a, nau'rar tantance masu zabe da makamantan su.

KARANTA KUMA: Kashe fiye da N1bn yayin yakin zabe - An maka Buhari da Atiku gaban Kuliya

Majiyar jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, neman aiwatar da duk wani bincike kan kayayyakin da aka ribata wajen gudanar da kowane zabe na tabbata biyo bayan sahalewa da kuma amincewar kotun daukaka kara.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, akwai za a yi watsi da cancantar takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa biyo bayan maka su gaban kuliya a sanadiyar yadda kowanen su ya kashe fiye da Naira Biliyan 1 yayin gudanar yakin su na neman zabe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel