Sarkin Musulmi, manyan sarakunan gargajiya, sun kaiwa Buhari ziyara

Sarkin Musulmi, manyan sarakunan gargajiya, sun kaiwa Buhari ziyara

Kungiyar sarakunan gargajiya Najeriya a ranan Talata sun kaiwa shugaba Muhammadu Buhari ziyarar taya murna kan nasararsa akan zaben shugaban kasa.

Shugaban kungiyar kuma mai alfarma sarkin Musulmi, Saad Abubakar na uku, ya bayyana ra'ayinsa inda yace nasarar Buhari kaddara ce kawai daga Allah kuma kada wanda ya kalubalanci haka.

Yace: "Nasararka a zaben shugaban kasa karo na biyu a daukeshi a matsayinn abinda Allah ya kaddara kuma babu wani ma'alukin da zai iya canza kaddara."

"Sakamakon zaben abune daga Allah kuma saboda haka, muna kira ga kowa su mara maka baya wajen samar da zaman lafiya, cigaba, gyaran kasarmu."

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: EFCC ta saki lauyan PDP, Tanimu Turaki

A bangare guda, Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Sokoto ta nisanta kanta daga jita-jitan cewa tana shirin tsige Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, idan har ta lashe zaben gwamna.

Shugaban jam’iyyan, Isa Sadiq Acida, ya bayyana hakan ne ga yan jarida jiya a Sokoto.

Yace jam’iyyar adawa ce tayi wannan kulle kullen, ta kuma yi hakan ne domin batanci ga martaban wassu mutanen kirki da aka alakanta ga wannan ikirarin.

"Tabbatacce Sultan ne uba ga dukkan musulmai kuma mun kasance masu rungumar darajojin al’adunmu da addinin mu,” a cewar Acida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel