Mun yi aringizon kuri’u a zaben bana inji wani ‘Dan Jam’iyyar APC

Mun yi aringizon kuri’u a zaben bana inji wani ‘Dan Jam’iyyar APC

Akwai alamu da ke nuna cewa jam’iyyar APC mai mulki ta tafka magudi na Inna-naha a zaben shugaban kasa da kuma ‘yan majalisun tarayya da aka yi makonni 2 da su ka wuce a Jihar Kano da fadin Najeriya.

Mun yi aringizon kuri’u a zaben bana inji wani ‘Dan Jam’iyyar APC
An ji faifan da ke bayanin yadda Jam’iyyar APC ta murde zaben Kano
Asali: Twitter

Mun samu wannan labari ne ta wani faifan murya inda aka ji wani da ake tunani cewa yana cikin manyan APC a jihar Kano yana bayyanawa wani Abokin sa yadda su ka murde zabukan da aka yi a wasu kananan hukumomi.

A sautin wayar da aka dauka, wani babban ‘dan APC da ake ikiarin sunan sa Honarabul Kamilu, an ji yadda APC ta murde kuri’un yankin Doguwa, Tudun Wada, Kumbotso, Kunci, Shanono, Bagwai, da kuma Dawakin Tofa, da sauran su.

Wannan babban ‘dan APC yake bayyanawa wani Bawan Allah da su ke waya cewa duk aringizo su kayi domin a tika PDP da kasa. Jam’iyyar PDP dai ta gaza kawo ko da kujera guda a zaben ‘yan majalisa 24 da kuma Sanatocin jihar.

KU KARANTA: Wadanda ke neman kujerar Ganduje sun gana da Kwankwaso

Da bakin sa, wannan mutumi yake cewa sun sa an rike sakamakon zaben da aka yi a yabkin karamar Hukumar Nassarawa, Tarauni, Dala da karamar hukumar Birnin Kano ne da nufin a ba shugaba Buhari kuri’u kamar miliyan 2.

A karshe dai hakan bai yiwu ba, inda shugaba Muhammadu Buhari ya tashi da kuri’u sama da miliyan 1.4. Buhari ya ba ‘dan takarar PDP, Atiku Abubakar, ratar kuri’a fiye da miliyan guda a zaben, wanda ya sa PDP tace za ta tafi Kotu.

A karshen wayar an ji wannan mutumi yana fadin yadda APC ta ci kujerar Sanatan Kano ta tsakiya da aringizo. An dauko muryar Hon. Kamilu yana cewa: “Wallahi tallahi an karawa Shekarau kuri’a 200, 000”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel