Jam’iyyu 32 da ‘yan takara 20 sun goyi bayan PDP domin kayar da gwamna Abubakar

Jam’iyyu 32 da ‘yan takara 20 sun goyi bayan PDP domin kayar da gwamna Abubakar

Jam’iyyu 32 da ‘yan takarar gwamna 20 ne su ka dunkule wuri guda tare da goya wa jam’iyyar PDP baya da dan takarar ta na gwamna, Sanata Bala Mohammed, domin ganin an hada karfi da karfe domin kayar da gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar, da ke takara a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Wannan shine karo na uku da jam’iyyun adawa da ma su ruwa da tsaki ke yunkurin ganin sun kayar da jam’iyyar APC da dan takarar ta.

A cewar shugaban gamayyar jam’iyyun, Bello Kirfi, sun yanke shawarar goyon bayan jam’iyyar PDP ne bayan kamala wata tattauna da su ka yi yau, Talata, a Otal din River Edge, da ke Bauchi.

Kirfi ya ce daga cikin jam’iyyun da su ka shiga hadakar da su ka yi da PDP su ne; United Progressive Party (UPN), Change Advocacy Party (CAP), All Peoples Movement (APM), All Blendin Party (ABP), Action Joint Alliance (AJA), Advance Peoples Democratic Alliance (APDA), Grassroots Development Party of Nigeria (GDPN), da Accord Party (AP).

Jam’iyyu 32 da ‘yan takara 20 sun goyi bayan PDP domin kayar da gwamna Abubakar
Mohammed Abubakar
Asali: Depositphotos

Ragowar sun hada da; ID, AGAP, NGP, NPC, LPN, MDP, NPM, PPC, PT, AAP da ANP da wasu da dama.

Kirfi ya bayyana cewaer sun dunkule wuri guda ne a kokarinsu na ganin dan takara mai nagarta ya kayar da gwamna mai ci a zaben da za a yi ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Ya bukaci jama’ar jihar Bauchi da ma su ruwa da tsaki su goyi bayan Sanata Bala Mohammed.

DUBA WANNAN: Buhari ya karbi bakuncin mambobin kwamitin kamfen din sa, hoto

Ya kara da cewa jama’ar jihar Bauchi na ganin mutunci da kimar shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma hakan ne ya say a samu kuri’u ma su yawa daga jihar amma “ba don mu na farinciki da halin da mu ke ciki a jihar Bauchi ba.”

Da ya ke karbar ‘yan takarar da jam’iyyun, Sanata Bala Mohammed, wanda Abubakar Kari ya wakilta ya nuna jin dadi tare da yin godiya ga Kirfi.

Da ya ke mayar da martini a kan wannan lamari, sakataren yada labaran gwamnan Bauchi ya ce yin hadakar ba zai girgiza gwamnan ba ko kadan.

A cewar sa, “babu wata jam’iyyar adawa a jihar Bauchi, ka tambayi ma su kada kuri’a za su fada ma ka cewar ba su san wata jam’iyya ba bayan jam’iyyar APC.

“Zaben ranar Asabar zai raba gardama tsakanin gwamna Abubakar da ragowar ‘yan takarar da aka rasa abun da za a tallata su da shi.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel