Obasanjo ya yi magana kan abunda ke tsakaninsa da Buhari bayan zaben Shugaban kasa

Obasanjo ya yi magana kan abunda ke tsakaninsa da Buhari bayan zaben Shugaban kasa

Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Talata, 5 ga watan Fabrairu yace ba zai taba daina sukar gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba har sai Shugaban kasar yayi abunda ya kamata a gwamnatin.

Tsohon Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin bikin cikarsa shekaru 82 a duniya wanda aka gudanar a dakin karatunsa da ke Abeokuta, babbar birnin jihar Ogun.

Obasanjo na martani ne ga sakon Alake kuma sarkin Egbaland, Oba (Dr.) Adedotun Aremu Gbadebo wanda ya bukaci Cif Olusegun Obasanjo da ya kyale Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya samu damar mayar da hankali ga ayyukan gwamnati.

Obasanjo ya yi magana kan abunda ke tsakaninsa da Buhari bayan zaben Shugaban kasa
Obasanjo ya yi magana kan abunda ke tsakaninsa da Buhari bayan zaben Shugaban kasa
Asali: Facebook

A cewar jigon kasar, shugabanci ba lamari bane na iyalai, inda ya kara da cewa damokardiya ta gaji suka da yaba wa a kan kowani lamari.

KU KARANTA KUMA: Ka daina sukar Buhari, ka nema wa kanka hutu a shekara 82 - Alake ya shawarci Obasanjo

"Babu wani abu na daban tsakanina da shugaba Buhari.

"A damokradiyya, kana iya sukar wata manufa, ko gwamnati ko kuma wani shugaba saboda damokradiya ba lamari na iyali bane.

"Idan dan uwana ne ke shugabanci sannan naga yana aikata abunda ba shi nake gani ya kamata yayi ba, dole a soke shi haka damokradiya ta kunsa.

"Na dade a wannan matsayin fiye da dadewar da duk wani dan Najeriya zai yi.

"Don haka idan nace wani a gwamnatin Najeriya bai yi kokari ba, toh wannan gwamnatin ta tabbatar da cewar tayi," cewar shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel