Da-na-sani: Mun yi nadamar zabar Atiku akan Buhari - Wasu 'yan Arewa

Da-na-sani: Mun yi nadamar zabar Atiku akan Buhari - Wasu 'yan Arewa

Wasu 'ya'yan jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Yobe dake a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya sun sanar da sauya shekar su a siyasance ya zuwa jam'iyyar da ke mulki a jihar ta All Progressives Congress (APC).

Haka ma dai da shugaban 'yan siyasar da suka sauya sheka ke jawabi a karamar hukumar Fika inda aka karbe su a yayin wani taron gangamin yakin neman zabe, Alhaji Ahmadu Usman ya bayyana cewa shi da mutanen sa sun yi nadamar zabar Atiku a zaben da ya gabata.

Da-na-sani: Mun yi nadamar zabar Atiku akan Buhari - Wasu 'yan Arewa
Da-na-sani: Mun yi nadamar zabar Atiku akan Buhari - Wasu 'yan Arewa
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Yan kabilar Ibo sun nuna zalamar su ga kujerar Saraki

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa daga nan ne kuma sai ya jadda goyon bayan su ga irin salon mulkin da jam'iyyar ta All Progressives Congress (APC) ke gudanarwa a jihar sannan kuma ya sha alwashi a madadin mabiyansa cewar za suyiwa jam'iyyar aiki a zabe mai zuwa.

Haka ma dai duk dai a jihar ta Yobe wasu shugabannin jam'iyyar PDP a kananan hukumomin ta 17 duk sun sauya sheka ya zuwa APC.

Wannan dai na zuwa a dai dai lokacin da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar yake kalubalantar sakamakon zaben da ya gudana da hukumar zabe tace ya sha kaye a hannun shugaba Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel