Kashe fiye da N1bn yayin yakin zabe - An maka Buhari da Atiku gaban Kuliya

Kashe fiye da N1bn yayin yakin zabe - An maka Buhari da Atiku gaban Kuliya

'Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar NRM, National Rescue Movement, ya yi karar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a gaban kuliya kan sabawa dokar kasa yayin gudanar da yakin su na neman zabe.

Mista Usman Ibrahim Alhaji, daya daga cikin wadanda suka fafata yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu, ya nemi hukuncin shari'a ya tabbata akan manyan 'yan takarar biyu sakamakon yadda suka yiwa dokar kasa Karan tsaye a zaben bana.

Kashe fiye da N1bn yayin yakin zabe - An maka Buhari da Atiku gaban Kuliya
Kashe fiye da N1bn yayin yakin zabe - An maka Buhari da Atiku gaban Kuliya
Asali: UGC

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Mista Ibrahim ya maka shugaban kasa Buhari da kuma Atiku a gaban Kuliya sakamakon yadda suka kashe fiye da Naira biliyan 1 wajen gudanar da yakokin su na neman zaben kujerar shugaban kasa.

Biyo bayan yadda kowane daya daga cikin manyan 'yan takarar biyu suka sabawa dokokin hukumar zabe wajen batar da wannan dukumar dukiya yayin gudanar yakin su na neman zaben bana, Ibrahim-Alhaji ya nemi kotu ta ribaci hukunci da kuma tanadin sashe na 91 cikin dokokin zaben kasar nan.

KARANTA KUMA: Zaben 2019: Ba za mu hana Atiku shigar da kara ba - APC

'Dan takarar na jam'iyyar NRM, ya nemi kotun ta yi watsi da cancantar takarar shugaban kasa Buhari da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa sakamakon rashin da'a da kuma sabawa tanadin dokokin zaben kasar nan da aka shimfida a shekarar 2010 da ta gabata.

Bayan nutsuwa domin sauraron Lauya mai shigar da wannan korafi, Mista Ezekiel Ofou, Alkalin babbar Kotun, Mai shari'a Ahmed Muhammad, ya daga sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Maris domin bayar da dama ta gabatar da cikakkun shaidu da hujjoji.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel