Zaben 2019: Ba za mu hana Atiku shigar da kara ba - APC

Zaben 2019: Ba za mu hana Atiku shigar da kara ba - APC

Jam'iyyar APC a yau Talata ta yi karin haske tare da bayyana matsayar ta kan yunkurin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, shigar da kara wajen neman hakkin sa a shari'ance biyo bayan babban zaben kasa.

Kakakin kungiyar yakin neman zaben kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Festus Keyamo, ya bayyana cewa jam'iyyar ba ta da wani nufi na hana Atiku neman hakkin sa a shari'ance biyo bayan babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019.

Zaben 2019: Ba za mu hana Atiku shigar da kara ba - APC
Zaben 2019: Ba za mu hana Atiku shigar da kara ba - APC
Asali: Depositphotos

A yayin da ake ci gaba da shawarta gami da kiraye-kirayen hana Atiku shigar da kara gaban Kuliya dangane da rashin amincewa da sakamakon babban zabe, jam'iyyar APC ta yi karin haske da cewar ba ta da hannu cikin neman Atiku ya dauki dangana ko kuma rungumar kaddara kan yadda sakamakon zaben ya kasance.

Da yake ci gaba da zayyana kalaman sa cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a babban birnin kasar nan na tarayya, Mista Keyamo ya ce a halin yanzu jam'iyyar APC ta kosa Atiku ya yi gaggawar shigar da korafin sa gaban kotu inda ta ke cewa 'ga mai fili ga mai Doki'.

KARANTA KUMA: Zaben 2019: PDP za ta kai ƙarar APC wajen Majalisar dinkin Duniya

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyoyi da dama da kuma masu fada a ji na kasar nan, na ci gaba da kiraye-kiraye tare da shawartar Atiku kan daukar dangana da kuma riko da kaddara biyo bayan rashin nasarar sa zaben bana.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, a jiya Litinin, 'yan takara 12 masu hankoron kujerar shugaban kasa sun taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar samun nasarar tazarce yayin zaben kasa da aka gudanar makonni biyu da suka gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel