Zaben gwamnoni: Jam’iyyu 49 da ‘yan takara 32 sun janye wa El-Rufa’i a Kaduna

Zaben gwamnoni: Jam’iyyu 49 da ‘yan takara 32 sun janye wa El-Rufa’i a Kaduna

Wasu gungun ‘yan takarar kujerar gwamna a jihar Kaduna da su ka kira kan su ‘ma su son cigaba’ sun bayyana cewar sun janye takarar su tare da mara wa dan takarar jam’iyyar APC kuma gwaman jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, baya a zaben da za a yi ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

‘Yan takarar sun bayyana wa jama’a wannan mataki da su ka dauka a jiya, Litinin, bayan kamala wani taro da su ka yi.

Shugaban jam’iyyar UDP, Kwamred Auwal Abdullahi, ya ce sun goya wa El-Rufa’i baya ne domin bashi damar cigaba da aiyukan alheri da ya fara a jihar.

Da aka tambaye shi ko ta yay a goyon bayan su zai taimaka wa El-Rufa’i, ganin cewar dukkan jam’iyyun su kananu ne da jama’a ba su san su ba, sai Abdullahi ya ce, “mu na da na mu magoya bayan.”

Zaben gwamnoni: Jam’iyyu 49 da ‘yan takara 32 sun janye wa El-Rufa’i a Kaduna
Jam’iyyu 49 da ‘yan takara 32 sun janye wa El-Rufa’i a Kaduna
Asali: Twitter

Abdullahi ya kara da cewa El-rufa’i ya yi kokarin da ya kamata a goya ma sa baya ya kai ga nasara a zaben gwamnoni da mambobin majalisar wakilai.

Mun dade mu na tuntuba kafin yanke wannan hukunci kuma mun yi hakan ne saboda kishin jihar Kaduna da mu ke da shi. Mun san ba za mu iya cin zabe ba, a saboda haka ne mu ka yanke shawarar hada karfin mu wuri guda domin goya wa dan takarar da mu ke da masaniyar cewar ya na da kishin jihar Kaduna da jama’ar ta.

DUBA WANNAN: Kisan mutane 66 a Kaduna: El-Rufa'i ya ziyarci kauyukan karamar hukumar Kajuru

“Ba wai mu na duba bukatun kan mu ne, mu na duba jihar Kaduna ne da jama’ar ta,” a cewar Abdullahi.

Jam’iyyun da ‘yan takarar sun ce duk da sun a da manufofi daban-daban, sun jingine duk wani banbanci gefe guda domin ganin jihar Kaduna ta samu shugabanci nigari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel