Sanata Akpabio ya fi karfin faduwa zabe – Inji Shugaba Buhari

Sanata Akpabio ya fi karfin faduwa zabe – Inji Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashi takobin cewa sai jam’iyyar APC ta kwato kuri’un da aka yi zargin sace mata a lokacin zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya a jihar Akwa Ibom.

Buhari ya yi wannan jawabi ne a wani taron ganawa da al’ummar jihar Akwa Ibom, a wata ziyarar godiya da ya je yi dangane da zaben sa da suka yi a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa jam’iyyar APC ta fadi dukkanin zabukan da aka gudanar a jihar Akwa Ibom.

Ba ta ci kujerar sanata ko ta majalisar tarayya ko daya ba. Haka kuma ba ita ce ta samu kuri’u mafi rinjaye a zaben shugaban kasa ba. Duk PDP ce ta ashe zabukan.

Sanata Godwill Akpabio ya fadi zaben sanata, sai dai kuma ya ce magudi aka yi masa.

Sanata Akpabio ya fi karfin faduwa zabe – Inji Shugaba Buhari
Sanata Akpabio ya fi karfin faduwa zabe – Inji Shugaba Buhari
Asali: Depositphotos

APC ta yi ta rakadin cewa ta na neman a cire Kwamishinan Zabe na Jihar Akwa Ibom, Mike Igini.

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ne ya wakilci Buhari a taron ziyarar nuna godiyar jiya Litinin a Uyo, babban birnin jihar Akkwa Ibom, inda ya yi kira ga magoya bayan APC su yi zaben gwamna, kuma su kare kuri’un su.

Osinbajo ya nuna tsananin rashin jin dadin yadda Akpabio ya fadi zaben sanata.

Ya yi zargin cewa INEC ce ta kayar da shi.

Ya yi wa jama’ar jihar alkawarin cewa sai sun shawo kan dukkan kuri’un da aka yi wa Akpabio da sauran ‘yan takara a jihar fashinsu.

“Abin da aka yi wa Akpabio a zaben sanata fashi da makami ne da rana tsaka.

“Ba zai taba yiwuwa Sanata Akpabio ya fadi zabe ba. Ba mu da wata tantama cewa Sanata Akpabio ne ya ci zaben sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.

“Ni da Adams Oshiomhole mun fi karfin faduwa zabe. Domin mun dade mu na adawa, don haka ba mai iya sake kayar da mu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An gurfanar da Dino Melaye yan kwanaki bayan lashe zabensa

Ya roki jama’a su zabi Mista Ekere, dan takarar gwamna na APC, wanda zai gwabza takara da Gwamna Udom Emmanuel na PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel