Siyasar Najeriya: Abin da ya sa Shugaba Buhari ya doke Atiku

Siyasar Najeriya: Abin da ya sa Shugaba Buhari ya doke Atiku

A Ranar 23 ga Watan jiya ne aka yi zaben shugaban kasa a Najeriya, inda shugaba Muhammadu Buhari ya samu damar zarcewa a kan kujerar sa bayan ya doke Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da wasu tarin ‘yan takara a kasar.

Siyasar Najeriya: Abin da ya sa Shugaba Buhari ya doke Atiku
Zargin da ke kan Atiku ya taimakawa Buhari wajen cin zabe
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times tayi nazari ta kawo duk wasu dalilai da ake tunanin sun taimaka wajen samun nasarar Muhammadu Buhari a zaben na wannan karo. Mun tsakuro wasu daga cikin wannan dalilai:

1. Kuri’un ‘Yan Arewa

Tun 2003 lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake takara, jihohi da daman a Arewa irin su Sokoto, Yobe, Borno, Gombe, da Bauchi, su ke tare da shi komai runtsi. Wannan karo irin wadannan jihohi ba su yi wa APC kasa a gwiwa ba duk da cewa kokarin bai kai na 2015 ba.

2. Karfin mulki

Wani abu da ya taimakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne karfin karagar mulki da yake kai. A 2015 ne dai karon farko da shugaba mai-ci ya sha kasa a zaben Najeriya. Wannan ya taimakawa shugaba Buhari samun kaso mai tsoka a kusan duka jihohin da ke Najeriya.

KU KARANTA: 2019: Ana lallashin Atiku ya fasa maka INEC da Buhari a Kotu

3. Alakar Buhari da sauran Gwamnoni

Shugaba Buhari yana da kyakkyawar alaka tsakanin sa da gwamnonin Kudu da Gabas maso Kudancin Najeriya, wadanda ba su cikin tafiyar APC. Buhari bai taba nuna masu banbancitun da ya fara mulki ba. Wannan ya hana su fitowa su yake sa a 2019 domin PDP ta samu ta ci zabe.

4. Lissafin Jam’iyyar APC

Jam’iyyar APC mai mulki tayi kokari wajen jawo wasu manyan ‘Yan PDP da ke Kudancin Najeriya domin ragewa jam’iyyar adawar karfi a yankin. Tasirin wadannan ‘yan siyasa ya nakasa PDP a jihohi irin su Akwa-Ibom, Ribas, Ebonyi, har da Abia. (inda APC ta samu Sanata)

5. Zargin da ke wuyan Atiku

Zargin satar dukiyar jama’a da ke kan Atiku Abubakar, wanda PDP ta ba tuta a zaben na 2019 yana cikin abin da ya taimakawa Buhari cin zabe. APC tayi amfani da gaskiyar Shugaba Buhari da kuma irin barnar da PDP ta tafka a baya wajen samun nasara a zaben na wannan karo.

Kamar yadda binciken ya nuna, sauran dalilan da su ka asassa galabar shugaba Buhari sun hada da dakatar da zaben da aka yi da kuma iricin rikicin cikin gidan da ake yi a PDP har gobe a jihohi irin su Ekiti, Osun, Kano, Borno da kuma yankin Kasar Ibo inda Abokin takarar Atiku ya fito.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel