Na'urorin tantance katin zabe 63 sunyi batar dabo a Bayelsa

Na'urorin tantance katin zabe 63 sunyi batar dabo a Bayelsa

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC reshen jihar Bayelsa ta yi kira ga wadanda ke rike da na'urorin tantance katin zabe (Card Reader) 63 da suka bace su dawo da su kafin ranar Asabar da ayi zabe.

A jiya Litinin ne hukumar ta sanar da cewa 63 cikin na'urorin tantance katin zabe da akayi amfani da su yayin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya sun bace.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa shugaban sashin wayar da kan masu zabe na INEC, Wilfred Ifogah ya ce anyi amfani da na'urorin ne a kananan hukumomin Brass, Sagbama, Nembe, Ijaw ta Kudu da Yenagoa.

DUBA WANNAN: Cin amana: An kama wani sufeton 'yan sanda na taimakawa 'yan daba yin basaja

Na'urorin tantance katin zabe 63 sunyi batar dabo a Bayelsa
Na'urorin tantance katin zabe 63 sunyi batar dabo a Bayelsa
Asali: Facebook

Ifogah ya ce a gudama ta 6 rumfar zabe ta 19 da ke Brass, Card Reader daya ya bace, 24 sun bace a gundunar Nambe a rumfunan zabe na 1, 4, 12 da 13 yayin da 24 sun bace a Ijaw ta Kudu a rumfunan zabe na 1, 2, 3, 12 da 15.

"Yes, kimanin Card Reader 63 ne suka bace. Baturen zabe na jihar, Mr Monday Udom ya fitar da sanarwa in da ce duk wadanda ke rike da su su mayarwa INEC kafin ko ranar Laraba," inji shi.

"Card Reader takwas sun bace a Sagbama, rumfar zabe na 5, 6 da 3, yayin da guda shida sun bace a Yenagoa a rumfar zabe na 1, 11 da 16."

An ruwaito cewa Ifogah ya jiyo kwamishinan zaben yana cewa ba za a hukunta wadanda suke rike da na'urorin ba idan sun dawo da su.

A ranar 9 ga watan Maris ne za a gudanar da zabukkan gwamna da 'yan majalisun jiha a kasar amma a jihar Bayelsa zaben 'yan majalisun jiha kawai za a gudanar saboda wa'adin Gwamna Seriake Dickson za ta kare ne a shekarar 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel