Yanzu yanzu: Jagororin PDP sun mamaye shelkwatar INEC kan zaben shugaban kasa

Yanzu yanzu: Jagororin PDP sun mamaye shelkwatar INEC kan zaben shugaban kasa

Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa jagororin jam'iyyar PDP a halin yanzu na ci gaba da yin zanga-zanga a shelkwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a Abuja, bisa zaben shugaban kasa da na 'yan majaisun tarayya da aka kammala.

Uche Secondus, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, ya jagorancin dubunnan magoya bayan jam'iyyar inda suka mamaye ofishin hukumar da ke Maitama, da misalin karfe 3 na rana.

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sha kasa a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC da tazarar sama da kuri'u miliyan hudu.

KARANTA WANNNAN: Ana daf da zabe: INEC ta cire APC daga yin takarar gwamnan jihar Enugu

Yanzu yanzu: Jagororin PDP sun mamaye shelkwatar INEC kan zaben shugaban kasa
Yanzu yanzu: Jagororin PDP sun mamaye shelkwatar INEC kan zaben shugaban kasa
Asali: Twitter

Sai dai jam'iyyar PDP ta ki amincewa da sakamakon zaben wacce tare an tafka magudi a cikinsa.

Jagororin PDP da mambobinci a yanzu haka na ci gaba da rera wakoki a gaban shekwatar hukumar INEC duk da kasancewar akwai jami'an tsaro a gaban ofishin hukumar.

Cikakken labarin yana zuwa...

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel