Zaben 2019: Mu ne mu kayi nasara - Buba Galadima

Zaben 2019: Mu ne mu kayi nasara - Buba Galadima

- Injiya Buba Galadima ya yi ikirarin cewa dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ne ya lashe zaben shugabancin kasa na 2019

- A cewar Buba Galadima, jam'iyyar na PDP tana da kwararan hujjoji da za ta gabatar a gaban kotu da zai nuna cewa Atiku ne ya lashe zabe

- Buba Galadima ya kuma yi ikirarin cewa wasu na kokarin hana su zuwa kotu domin jam'iyyar APC na tsoron hujojin da za su gabatar

Tsohon na hannun daman Shugaba Muhammadu Buhari kuma daya daga cikin masu magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, Injiniya Buba Galadima ya ce jam'iyyar PDP tana goyon Atiku a kan matakin da ya dauka na zuwa kotu domin kallubalantar sakamakon zaben 2019.

Jam'iyyar PDP da Atiku Abubakar sun ce ba su amince da sakamakon zaben 2019 da Hukumar Zabe INEC ta fitar ba inda su kayi ikirarin cewa an tafka magudi a zaben.

Mu ne muka lashe zaben 2019 - Buba Galadima
Mu ne muka lashe zaben 2019 - Buba Galadima
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Radadin kaye: Masoyin Atiku ya hana wani mabaraci sadaka (Bidiyo)

INEC ta sanar da cewa Shugaba Buhari ya lashe zaben ne inda ya samu kuri'u 15,191,847 kuma ya lahe zabe a jihohi 19 na kasar.

A cewar Buba Galadima, sun cimma matsayar zuwa kotu ne bayan da suka yi wata doguwar tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a ranar Litinin da ta gabata.

Ya ce suna da hujjoji da za su gabatarwa kotu da zai nuna cewa "mu ne muka lashe zabe. Saboda haka, dole a bai wa dan takarar shugabancin Najeriya," inji shi.

Kazalika, Buba Galadima ya yi ikirarin cewa akwai wasu ta ke yiwa dan takarar na PDP matsin lamba a kan niyyarsa ta zuwa kotu domin kallubalantar sakamakon zaben inda ya ce hakan ne faruwa saboda APC na tsaron hujjojin da za su gabatar a kotu.

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa kasahen Ingila, Amurka, Faransa da wasu kasahen duniya duk sun aike da sakon taya murna ga shugaba Muhammadu Buhari tare da yin ammana kan yadda aka gudanar da zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel