Ana daf da zabe: INEC ta cire APC daga yin takarar gwamnan jihar Enugu

Ana daf da zabe: INEC ta cire APC daga yin takarar gwamnan jihar Enugu

- Jam'iyyar APC ba za ta gabatar da d'an takara ba a zaben gwanan jihar Enugu da za a gudanar a ranar Asabar 9 ga watan Fabreru

- Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja, ta kori Sanata Ayogu Eze a matsayin dan takarar gwamnan jihar Enugu karkashin jam'iyyar APC

- Sai dai APC wacce ta bayyana Ayogu a matsayin dan takarar da ta sani, ta gaza bin umurnin kotu, na sanya sunan Ogara a matsayin dan takarar gwamnan jihar

Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa jam'iyyar APC ba za ta gabatar da d'an takara ba a zaben gwanan jihar Enugu da za a gudanar a ranar Asabar 9 ga watan Fabreru. Bisa jaddawalin sunayen 'yan takara da hukumar zabe ta kasa INEC ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ya nuna cewa APC ba ta da d'an takara a zaben jihar.

Kundin sunayen 'yan takarar wanda ke dauke da sa hannun Rose Oriaran-Anthoy, sakataren hukumar INEC, ya ce hakan ya faru ne bisa kokarin hukumar na bin umurnin da kotu ta bayar, bayan da jam'iyyar ta gaza gabatar da sabon sunan dan takarar gwamnan sakamakon korar Ayogu.

KARANTA WANNNAN: Wani matashi ya kashe makwabciyarsa saboda ta tambaye shi ranar da zai yi aure

Ana daf da zabe: INEC ta cire APC daga yin takarar gwamnan jihar Enugu
Ana daf da zabe: INEC ta cire APC daga yin takarar gwamnan jihar Enugu
Asali: Depositphotos

A cikin kundin sunayen 'yan takarar mai shafuka 330, Enugu ta mamaye shafi na 100 zuwa na 111, inda babu sunan dan takarar jam'iyyar APC a cikin jerin 'yan takarar.

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja, ta kori Sanata Ayogu Eze a matsayin dan takarar gwamnan jihar Enugu karkashin jam'iyyar APC.

Sai dai ko a baya bayan nan, kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC, wanda a baya ya bayyana Ayogu a matsayin dan takarar da jam'iyyar ta sani, ta gaza bin umurnin kotu, na sanya sunan Ogara a matsayin dan takarar gwamnan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel