Tuhuma: Hukumar EFCC ta sakan ma tsohon dan takarar shugaban kasa mara

Tuhuma: Hukumar EFCC ta sakan ma tsohon dan takarar shugaban kasa mara

Hukumar EFCC ta sanar da sakin wani jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Tanimu Turaki, babban lauyan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, kuma mataimakin yakin neman zaben Atiku na mukamin shugaban kasa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Litinin, 4 ga watan Maris ne EFCC ta cafke Turaki, wanda ya nemi takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, amma Atiku ya kadashi, sa’annan ya taba zama ministan ayyuka na musamman a gwamnatin Jonathan.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: Jami’an EFCC sun yi ram da tsohon dan takarar shugaban kasa, Turaki

Tuhuma: Hukumar EFCC ta sakan ma tsohon dan takarar shugaban kasa mara
Turaki
Asali: Twitter

Kaakakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ne ya tabbatar da EFCC ta kama Kabiru cikin wata sanarwa daya fitar a tsakar daren Litinin, inda yace hukumar ta gayyaci Kabiru ne a ranar Litinin, inda ya amsa gayyatar da tayi masa.

“An kama Tanimu Turaki ne a lokacin da EFCC ta gayyaceshi don ya tsaya a matsayin wanda zai samar da beli ga surukin Atiku Abubakar, kuma daraktan kudi na kamfanin Atiku, Babalele Abdullahi, wanda EFCC ta kama a kwanakin baya.” Inji shi.

Sai dai majiya mai tushe ta ruwaito zuwa yanzu EFCC ta saki Babalele, sa’annan ta sako Tanimu Turaki, wanda tace ba tare da wani kwakkwara dalili aka kamashi ba.

Bugu da kari PDP tayi zargin kama tsohon Ministan na daga cikin manakisar da shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da jam’iyyar APC suke shirya ma jam’iyyar PDP da sauran abokan hamayya domin su lalata duk wani shiri da suke yin a kwatar mulki a gaban kotu.

Daga karshe kaakakin yace babu wani barazana da gwamnatin APC zata musu da zai sa su fasa zuwa gaban kotu don kwatar mulkin da yan Najeriya suka baiwa Atiku Abubakar amma aka danne masa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel